✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan leken asirin ’yan bindiga ya kashe kansa

Mai leken asirin ’yan ya kashe kansa a bayan sojoji sun kama Zamfara.

Wani mutum daga cikin ’yan leken asirin ’yan bindiga a Zamfara ya kashe kansa bayan sojoji sun kama shi a garin Dansadau na Karamar Hukumar Maru ta Jihar.

Wata majiya mai tushe a Dansadau ta shaida mana cewa sojoji sun kai samame a garin ne dauke da jerin sunayen wasu mutum 30 da ake zargin ’yan leken asirin ’yan bindiga ne.

“Lokacin da suka zo, sun rika bi gida-gida, sun kuma cafke duk wadanda sunayen ke cikin jerin wadanda ake zargin ’yan leken asirin ’yan bindiga ne, ciki har da mace daya.

“Bayan sun kama mutumin, wanda kuma sunansa ke cikin jerin ’yan leken asirin ’yan bindigar da ake neman, sai aka kai shi wani sansanin sojoji da ke yankin aka kulle shi a wani daki.

“To a lokacin da wani soja ya shiga dakin, sai mutumin ya yi maza ya kama bindigar sojan, yana kokarin kwace ta daga gare shi.


Gwamnatin Tarayya ta ce kwarya-kwaryar kasafin kudin 2021 da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar Litinin zai fara aiki nan take.

“Ana cikin haka ne wanda ake zargin ya yi matsa kunamar bindigar, ya yi harbi a kan wasu jarkokin man fetur kuma nan take wauta ta kama.

“Daga nan sai sojan ya yi sauri ya fice daga dakin ya bar wanda ake zargin wutar ta kama shi,” inji shi.

Mazauna garin sun shaida wa wakilinmu cewa akwai zargi mai karfi kan yadda wasu mazauna yankin suke mu’amalar kasuwanci da ’yan ta’addan.

Sun ce ana tuhumar wadanda ake zargin ne da laifin sayar da shanun sata da wayoyin sata da kuma baburan hawa ga ’yan bindiga.

“Ina iya nuna muku akalla matasa 11, yawancinsu ’yan Dansadau da suke harkar ’yan bindiga saboda miyagun sun yaudare su da kudade. Yanzu haka suna can tare da ’yan bindigar a sansanoni daban-daban a cikin dajin,” inji majiyar.

Mun nemi jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar Soji ta Operation Hadarin Daji a Jihar Zamfara, Kyaftin Ibrahim Yahaya, amma hakan bai samu ba har muka kammala hada wannan rahoton.