✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya rasu

Dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Nasarawa ta tsakiya, Alhaji Suleiman Adamu, ya rasu. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa dan…

Dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Nasarawa ta tsakiya, Alhaji Suleiman Adamu, ya rasu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa dan majalisar ya rasu ne a daren Alhamis, 30 ga watan Afrilu, a asibitin gwamanti da ke garin Keffi bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

Dan majalisa mai wakiltar Udege/Loko, Alhaji Mohammed Okpoku ne ya fitar da sanarwar hakan ranar juma’a, yana cewa za a yi jana’izarsa da safiyar ranar juma’a, 1 ga watan Mayu.

Alhaji Sulaiman Adamu ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar.