✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Birnin Kano Ya Sauya Sheka

Sauya shekar tasa, ta sanya mamabobin jam'iyyar APC a majalisar sun karu zuwa 20, yayin da PDP kuma ke da 11.

Dan majilisar dokoki mai wakiltar Karamar Hukumar Birni a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Salisu Ahmad Gwangwazo, ya sauya sheka zuwa APC, wanda hakan ya sa ’yan jami’yyar suka karu zuwa 20, PDP kuma ke da 11.

Bayanin hakan ya fito ne a wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar, Hamisu Chidari kamar yadda mai magana da yawun Kakakin majalisar Malam Uba Abdullahi ya bayyana.

“Ahmad Gwangwazo ya bayyana nuna bangaranci a jagorancin tshouwar jam’iyarsa ta PDP tun daga matakin kasa har zuwa jiha a matsayin dalilinsa na ajiye jam’iyar” a cewar Uba Abdullahi.

” kuma na taya Ahmad Gwangwazo murnar shigowa jam’iyarmu ta APC, kuma muna tabbatar masa cewa jamiyar ba za ta bar shi da sauran magoya bayansa a baya ba a dukkanin sha’aninta” in ji mai magana da yawun Kakakin majalisar.

Ya kuma ce jam’iyarsu na tafiya kan tsarin tafiya da kowa musamman a abubuwan da za su kawo cigaba ga jihar Kano.

“Hakan ne ma ya sa jamiyar APC za ta sake samun nasara a zabukan 2023” in ji shi.