✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Majalisar da ya yanke jiki a taron yakin neman zaben Tinubu ya rasu 

Dan majalisar ya yanke jiki ya fadi a lokacin kaddamar da yakin neman zaben Tinubu a Jos.

Wani dan Majalisar Dokokin Jihar Legas, Sobur Olayiwola Olawale ya riga mu gidan gaskiya bayan ya halarci taron kaddamar yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu. 

Bayanai sun ce Olawale wanda aka fi sani da Omititi mai wakiltar Karamar Hukumar Mushin II, na cikin ‘yan siyasar da suka halarci taron yakin neman zaben ranar Talatar nan a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, tun a yayin taron marigayin ya yanke jiki ya fadi kuma daga bisani ya ce ga garinku nan.

Wani jigo a jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa ko a karshen makon da ya gabata suna tare da Olawale.

“Mun hadu ne a gidan Sanata Ganiyu Olanrewaju Solomon (GOS) a ranar Lahadi, inda muka gaisa. Kuma a wancan lokacin yana cikin koshin lafiya.

“Koma mene ne amma da alamu mutuwarsa na da alaka da hawan jini. Amma mutuwarsa ta girgiza mu.”