✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan majalisar dokokin jihar Kogi ya rasu

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kogi, John Abah mai wakiltar Ibaji ya rasu ranar Laraba sakamakon rashin lafiya a wani asibiti a Birnin Tarayya, Abuja. Shugaban…

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kogi, John Abah mai wakiltar Ibaji ya rasu ranar Laraba sakamakon rashin lafiya a wani asibiti a Birnin Tarayya, Abuja.

Shugaban Jam’yyar APC a mazabar Kogi ta Gabas, Ahmed Omiattah ya sanar da rasuwar Dan Majalisar.

“Ina mika ta’aziyyarmu ga jama’ar Ibaji da kuma iyalan mamacin”, inji sanarwar daya fitar a garin Lokoja.

Rahotanni sun nuna dan majalisar ya jima yana kai komo a asibiti saboda rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

A sakon ta’aziyyarsa, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Mathew Kolawole ya bayyana rasuwar John Abba a matsayin babban rashi, la’akari da irin gudunmuwar da mamacin ke bayarwa a majalisar.

Sanarwarsa ta bakin saktare Yada Labarinsa, Femi Olugbemi ta mika ta’aziyya ga iyalan mamacin da ‘yan mazabar Ibaji game da rasuwar wadda ya ce ta haifar da babban gibi.