✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Bakori ya rasu a Saudiyya

Ya rasu a birnin Madinah.

Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, Honorabul Dokta Ibrahim Aminu Kurami ya rasu a Saudiyya.

Hon. Dokta Ibrahim Aminu Kurami ya rasu ne a kasa mai tsarki yayin da ya je aikin umara.

Dan Majalisar ya rasu ne bayan ’yar gajeruwar rashin lafiya da ya yi a birnin Madina da misalin karfe 2:00 na daren Litinin din nan.

Idan ba ku manta. ba an yi zabi Dan Majalisar ne a shekarar 2020 bayan rasuwar tsohon dan majalisar Honorabul Abdurrazak Ismail Tsiga a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar.