Dan Majalisar Wakilai, Suleiman Lere ya rasu | Aminiya

Dan Majalisar Wakilai, Suleiman Lere ya rasu

Suleiman Aliyu Lere, Dan Majalisar Wakilai.
Suleiman Aliyu Lere, Dan Majalisar Wakilai.
    Abubakar Muhammad Usman da Balarabe Alkassim

Majalisar Tarayya ta sake wayan gari da rashin daya daga cikin ’yan Majalisar Wakilai, a ranar Talata.

Hon. Sulaiman Lere, mai wakiltar Lere a Majalisar Wakilai, ya rasu bayan gajeriyar jinya a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, yana da shekara 53.

Takwaransa mai wakiltar Kudancin Kaduna, Mukhtar Ahmed ne ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar ta wayar tarho.

Rasuwar Lere ita ce ta shida da aka yi na ’yan majalisa tun daga shekarar 2019.

Idan ba a manta ba, dan majalisar mai wakiltar Bassa a Arewacin Filato, Haruna Maitala ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata, ya rasu ya bar yaro da wasu.