Daily Trust Aminiya - Dan Majalisar Wakilai Yuguda Hassan Kila ya rasu
Subscribe

Marigayi Yuguda Hassan Kila a zauren Majalisar wakilai (Hoto: )

Dan Majalisar Wakilai Yuguda Hassan Kila ya rasu

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yuguda Hassan Kila ya riga mu gidan gaskiya.

Dan Majalisar mai wakiltar Birnin Kudu/Buji daga Jihar Magaji Da’u Aliyu ne ya sanar da haka a ranar Alhamsi.

“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un. Ina sanar da ku game da rasuwar  Hon. Yuguda Hassan Kila, mai wakiltar Mazabar Tarayya ta Gwaram, Jihar Jigawa”.

Kafin rasuwarsa, Marigayi Hon. Kila shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Hukumar Kwastam.

Kazalika, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado Doguwa, ya tabbatar da mutuwar Honarabul Kila a zantarwar da ya yi da Aminiya ta wayar tarho

Ya ce “makonni biyu da suka gabata ne ya kwanta rashin lafiyar zazzabin cizon sauro mai tsanani, daga baya kuma rashin lafiyar ta rikide inda ya rika fuskantar karancin iskar Oxygen a cikin jininsa.”

More Stories