✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan mawaki Davido mai shekara 3 ya rasu

Ifeanyi mai shekara uku ya rasu bayan nutsewa a gidan mahaifinsa

Fitaccen mawakin Najeriya Davido, ya rasa dansa mai shekara uku, mai suna Ifeanyi, sakamakon nutsewa a ruwa.

Bayanai sun nuna Ifeanyi Adeleke ya rasu ne bayan ya nuste a ruwan ninkayar da ke gidan mahaifinsa da ke unguwar Banana Island a Legas a ranar Litinin, a lokacin Davido da budurwarsa, sun yi tafiya zuwa Ibadan domin halartar wani sha’ani.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Legas, Banjamin Hundeyin, ya shaida wa Aminiya a safiyar Talata cewa , “Gaskiya ne yaron ya rasu kuma muna binciken lamarin.

“Yanzu haka mutum takwas na amsa tambayoyi, duk wanda ake zargi yana da alaka da mutuwar zai amsa tambayoyi.”

Kawo yanzu Davido da mahifiyar Ifeanyi, wacce budurwar mawakin ce, ba su ce komai a kai ba.

Sai dai majiyar Aminiya ta ce mawakin ya kadu matuka da rasuwar, wanda hakan ya sa aka wuce da shi gidan mahaifinsa, daga asibitin da gawar yaron take.

Tuni mawaka da ke da kusanci da Davido suka yi ta tura sakonin alhininsu a shafukansu na sada zumunta.

Jarumar Nollywood, Eniola Badmus, ce dai ta fara wallafa sanarwar rasuwar dan a shafinta na Instagram, amma dai daga baya ta goge shi.

Fitattaun jaruman barkawanci da mawaka hadi da jaruman Nollywood irinsu Ayo AY Makun da Daddy Freeze da Lasisi Elenu sun mika ta’aziyyarsu ta shafukansu na Instagram, duk da cewa ba su fito karara sun bayyana wa suke yi wa ba.