✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Sa Kai Ya Rasu A Yayin Kai Dauki A Zariya 

’Yan bindiga sun halaka wani dan sa kai mai suna Kabiru Ibrahim mai shekaru 45 a lokacin da suka kai farmaki don dauke wani mutum…

’Yan bindiga sun halaka wani dan sa kai mai suna Kabiru Ibrahim mai shekaru 45 a lokacin da suka kai farmaki don dauke wani mutum a Unguwar Yarbawa da ke Gwargwaje a Karamar hukumar Zariya a daren ranar Juma’a.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, marigayin makwabci ne ga wanda maharan suka je sacewa kuma ya fito daga cikin gidansa ne domin kai dauki, amma ya cimma ajalinsa a sanadiyyar kwanton bauna da ’yan bindigar suka yi a kewayen gidan,  suka harbe shi a gadon baya a lokacin da ya gan su ya kuma juya don ya gudu.

Majiyar tamu ta kuma ruwaito Cewar ’yan bindigar za su kai 20 dauke da makamai kuma sun bi ta bayan katangar Kwalejin Kimiya da Kere-kere ta Nuhu Bamalli ne da ke makwabtaka da Unguwar.

Shi wanda aka je sacewa Allah ya taimake shi ba su sami yin tozali da shi ba, duk da sun shiga cikin farfajiyar gidansa amma ba su iya bude kofar shiga cikin gidan ba har jami’an tsaro suka isa Unguwar kuma ’yan bindigar suka tsere.

A cewar majiyar tamu, zuwan jami’an tsaro a wajen a kan lokaci ya taimaka kwarai domin maharan ba su sami yadda suke so ba.

Idan za a iya tunawa ko a cikin mako daya gabata ’yan bindiga sun dawo da cin kasuwarsu a yankin Wusasa da Gwargwaje inda suka dauki wani malamin Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Zariya a Unguwar Kuregu da ke Wusasa.

Bayanan da ke fitowa bayan aukuwar lamarin na nuni da yadda mutane ke wa sha’anin tsaro rikon sakainar kashi.

Rahotanni sun ce an ga wasu mutane da misalin karfe 8 na dare suna tambayar gidan Alhaji Bashir NEPA, kafin su dawo da dare don yin barnar tasu.

Mun tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Aliyu Jalige, wanda ya ce sun yi bako amma mu kira shi daga baya, sai dai kuma min kira amma wayar tasa ba ta tafiya.