✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda na barazana ga wakilin Daily Trust a Katsina

Wasu jami’an ’yan sanda sun yi barazanar yin kasa-kasa da wakilin kamfanin Daily Trust masu buga jaridar Aminiya na Jihar Katsina, Malam Tijjani Ibrahim a…

Wasu jami’an ’yan sanda sun yi barazanar yin kasa-kasa da wakilin kamfanin Daily Trust masu buga jaridar Aminiya na Jihar Katsina, Malam Tijjani Ibrahim a lokacin da yake tsaka da gudanar da aikinsa.

’Yan sandan sashen CTU sun yi wa Malam Tijjani barazanar ce a lokacin da yake kokarin daukar hoton manyan bakin da suka halarci taron bude wani gidan marayu da makaranta wanda Sanata Sadik ’Yar’aduwa ya gina.

Dan sandan na farko ya gargadi dan jaridar cewa kada ya kuskura ya dauki hoton, duk kuwa da tazarar da wakilin na Dailytrust ya bayar a lokacin da yake kokarin daukar hoton don kiyaye dokar ba da tazara a wajen taro.

Bayan Tijjani ya nuwa masa katinsa na shaidar aiki, kan ka ce kwabo sai wani dan sanda daga can gefe ya yunkuro ya bangaje dan jaridar; ya kuma yi kurarin zai yi kasa-kasa da shi a wurin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce suna bincike a kan lamarin.

Samun irin wannan barazanar ba bakon abu ba ne ga ’yan jarida daga jami’an tsaro.

A wasu lokutan ma har hana su gudanar da aikinsu ake yi, ko a kwace ko farfasa masu kayan aikin, ko ma a yi musu dukan tsiya.

Duk da cewa ’yan jarida kan hadu da irin wannan matsalar da jami’an sashen na CTU a wurare daban-daban, irin wannan furuci, musamman a Jihar Katsina inda ayyukan mahara suka yi kamari, kamata ya yi jami’in tsaron ya yi su ne a aikace yayin fuskantar ’yan bindiga, barayin shanu, da masu satar mutane ba wa a wajen taron da aka gayyato dan jaridar ya yi aikinsa ba.