✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya bindige direban tirela a Binuwai saboda ‘na goro’

An harbe direban ne a kan takaddama kan na goro

Wata sa-in-sa kan ba da na goro tsakanin wani dan sanda da direban tirela mai suna Aondohumba Terkula ta yi sanadin dan sandan ya harbe direban har Lahira, a titin Anyin da ke Karamar Hukumar Logon Jihar Binuwai.

Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce a daidai shingen binciken ‘yan sandan mai suna James Aondona ya tare direban wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Katsina-Ala.

James dai ya bukaci direban ya ba shi cin hancin N3,000,  inda shi kuma ya ce N1,500 kawai zai iya ba shi, kasancewar ba cikakken lodi ya dakko ba, abin da ya janyo musayar yawu tsakaninsu kenan har ya harbe shi.

Mutuwar direban dai ta harzuka sauran direbobin tirelolin da ke wajen, inda take suka rufe titin gami da dakatar da motoci daga wucewa tsawon sa’o’i, lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa.

To sai dai Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Catherine Anene, ta bayyana tsare dan sandan da ya aikata ta’asar, tare da ci gaba da bincike.

Dangane da gawar direban da aka harbe kuwa, ta ce tuni an mika ta ga babban Asibitin garin Katsina-Ala.