✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya harbe mutum 2 bayan ya yi mankas da giya

Dan sandan ya yi mankas da giya sannan ya shiga harbin mutane da bindiga.

Wani dan sanda ya harbe wasu mutum biyu bayan da ya yi mankas da giya a wajen wani casu da aka shirya a wata mashaya da ke rukunin gidaje na Gowon a Egbeda a Jihar Legas.

Lamarin ya faru a daren ranar Lahadi, wanda ya kawo karshen bikin murnar zagayowar ranar haihuwar da aka shirya, yayin da wadanda suka halarci taron suka tsere saboda fargabar kada su shiga hannun hukuma.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan dan sandan ya bugu da giya ne daga bisani ya bude wuta kan mahalarta taron.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce rundunar ta baza komarta don cafke dan sandan da ya ake zargin.

Ya ce, “Mun samu labarin cewa an yi harbe-harbe a wata mashaya a daren Lahadi kuma an kashe mutum biyu.

“Muna binciken lamarin da kuma wanda ya yi harbin. Ina tabbatar muku cewa wadanda suke da hannu a lamarin ba za su tsira ba.

“Za su fuskanci fushin Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas, CP Abiodun Alabi, saboda ba shi da hakuri akan irin wannan laifi, kuma tuni ya ba DPO yankin da abun ya faru umarnin yin gangami domin kamo wadanda suke da hannu.”

Rahotanni sun bayyana cewar Ifeanyi Asiwaju, wanda shi ne yake bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya gayyaci dan sanda wurin don samar musu da tsaro.

Wani matashi da ya wallafa bidiyon faruwar lamarin a shafinsa na Twitter @themannaman ya ce “’Yan sanda da aka kira don tabbatar da tsaro su ne suke harbin wadanda suka kira su don ba su tsaro… Najeriya ta yaya tsaro zai tabbata?

“Mai bikin ranar haihuwa ya gayyaci ’yan sanda domin tsaro. An ce dan sandan da ake zargin da aikata laifin ya bugu ne bayan shan giya, inda ya soma harbi sama, sannan ya harbe wasu.”