✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya ki karbar cin hancin N1m don sakin mai satar mutane a Kano

Kakakin ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani Alhaji Bamuwa Umaru mai shekara 62 a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna bisa laifin bayar da cin hancin Naira miliyan daya ga wani jami’in dan sanda.

Ana zargin mutumin ne da yunkurin bayar da cin hancin domin a saki wani Yusuf Ibrahim da aka kama kan zargin yin garkuwa da mutane.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce mutumin ya tunkari jami’in da ke kula da rundunar yaki da masu garkuwa da mutane a Jihar, SP Aliyu Mohammed, inda ya ba shi cin hancin domin a sako Ibrahim mai shekara 27 daga kauyen Danjibga da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

“Tawagar ‘Operation Restore Peace’ karkashin jagorancin CSP Usman Abdullahi, jami’in ’yan sanda da ke reshen Rijiyar Zaki a Kano ne suka kama wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne bayan wani direban da suka yi garkuwa da shi a hanyar Funtuwa zuwa Gusau ya gano shi, kuma ya karbi kudi Naira 500,000 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.

“A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa sannan ya kara da cewa ya ya yi garkuwa da mutane a kauyukan Sheme da Yankara da Faskari da Kucheri da ke cikin Jihohin Katsina da Zamfara.”

Kiyawa, ya ce Ibrahim ya kara da cewa ’yan kungiyarsu sun kashe kusan mutum 10 daga cikin wadanda suka sace kuma shi kadai ya kashe mutum biyu daga cikin wadanda suka sace.

Kakakin ya kara da cewa za su gurfanar da wanda ake zargin da mutumin da bayar da cin hancin a gaban kotu idan sun kammala bincike.