Dan sandan da ya harbi budurwarsa ya shiga hannu | Aminiya

Dan sandan da ya harbi budurwarsa ya shiga hannu

    Abbas Dalibi

Wani dan sanda mai mukamin Sajan da ya harbi  budurwarsa ya kuma tsere ya shiga hannu bayan mako uku yana wasan buya.

Ana zargin Sajan Eze Aiwansone na Sashen SPU shiyar Ikeja a Legas da harbin budurwarsa mai suna Joy Eze a baki, a yankin Opebi a Ikeja a ranar 7 ga watan Oktoba.

Kakain Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Legas, SP Abimbola Oyeyemi ya ce an kame wanda ake zargin ne da taimkom dan uwansa wanda shi ma dan sanda ne mai mukamin Insfekta.

“Yayansa wanda sufetan dan sanda ne shi ya kamo shi ya damka mana shi”, inji Muyiwa Adejobi.

Ya kara da cewa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na Rundunar na kara binciken lamarin.

Wani bidiyo ya karade shafukan zumunta ya nuna budurwar da raunin harbin bindigar a bakinta inda harsashi ya yi wa mukamukinta mummunan rauni.

Kazalika an sanya bidiyon ta a lokacin da aka garzaya da ita asibiti inda aka nuno ta a zaune tana jiran likitoci su ba ta kulawa.