Daily Trust Aminiya - Dan Sarki da ’yan mata hudu (2)
Subscribe

Dan Sarki da ’yan mata hudu (2)

A cikin mata hudun dan Sarki ya lura cewa ita babbar tana da son girma domin ya gwada kona mata kaya da dutsen guga har ta kwashe shi da mari.

Ta biyun kuma buri ya yi mata yawa kullum burinta shi ne ta auri dan Sarki amma kuma tana da yawan son maza ga yawo.

Ta ukun ba ta damu da auren dan Sarki ba ita dai mai karamar buri ce kuma ba ta da raini. Domin akwai ranar da ta yi ado za ta fita, dan Sarki kuma yana wanke mota sai ya watsa mata ruwa da gangan. Da ta fusata ta zage shi amma daga baya ta ba shi hakuri.

Ta hudun kuma ba ma za a sa ta a lissafi ba domin mata-maza ce. Sai son yin shigar maza da kuma wasa da maza.

Da dan Sarki ya koma gida sai ya gaya wa mahaifinsa cewa ya samu matar aure. Haka aka je gidan Hajiya Delu neman auren ’yarta ta uku. Aka yi aure. Sauran sun yi matukar nadama da ba su aikata abin da suka aikata da dan Sarkin ba.

More Stories