✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan shekara 6 ya harbe malamarsa

An ruwaito cewar malamar ta bata wa dalibin rai.

Jami’an tsaro a Jihar Virginia da ke Gabashin Kasar Amurka, sun ce wani dalibi dan shekara shida ya harbi malamarsa da bindiga.

Jaridar Newport News, ta ruwaito cewar babu dalibin da ya ji rauni a sanadin harbin bindigar da dalibin ya yi.

“Dalibin shekararsa shida, yanzu haka yana hannun jami’an tsaro a tsare,” cewar wani dan sanda, Steve Drew.

’Yan sanda sun ce wadda aka harba malama ce a makarantar kuma ana zargin ta bata wa dalibin rai je, wanda hakan ya sa ya zo da bindiga makarantar don daukar mataki.

Shugaban dakarun tsaron makarantar, George Parker, ya ce “Na tsorata matuka.

“Muna bukatar al’ummar da za su tabbatar da hana yara kanana samun bindiga.”

Harbin bindiga na ci gaba da zama barazana a Amurka, inda a watan Mayu, 2022 wani dan shekara 18 ya bude wa wasu dalibai wuta lamarin da ya yi sanadin mutuwar dalibai 19 da malamai biyu a Texas.

Kididdiga ta nuna cewar akalla mutum 44,000 ne suka mutu a sanadin harbin bindiga a Amurka.