✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan Sule Lamido ya zama dan takarar Gwamnan PDP a Jigawa

Ya sami nasara ne kan abokan takararsa su tara

Dan tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido ya yi nasarar samun tikitin takarar Gwamnan Jihar karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Baturen zabe daga hedkwatar jam’iyyar ya ce Mustapha ya samu nasara kan tsohon Minista a Ma’aikatar Ayyuka da kuri’a 829, sai kuma Alhaji Sale Shehu Hadejia.

Sai dai nasarar da Mustaphan ya samu ta kawo sabani a jam’iyyar domin wanda ya yi nasara kansa ya ta da jijiyoyin wuya dangane da yadda Mustaphan ya shigo filin wasa na Dutse in da aka yi zaben.

Tsohon Ministan dai ya yi wa shugaban jam’iyyar na jihar Alhaji Babandi Ibrahim Gule korafi kan kyale salon shigar da ya kira na fariya, har sai da aka shiga tsakani da ban-baki.

A nasa bangaren Mustapha Lamido ya mika godiya ga daliget din da suka zabe shi, tare da bayyana yadda zaben ya zamo irinsa na farko da matasan da suka fito takara sun dara na baya yarinta.

Tuni dai ragowar ’yan takarar da suka sha kaye suka yi alkawarin yin aiki tare wajen ganin jam’iyyar ta kai gaci a zaben mai zuwa.