✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Dan takarar Gwamnan Abiya na PDP ya rasu

Ya rasu bayan 'yar takaitacciyar jinya a Babban Asibitin Kasa da ke Abuja.

Dan takarar gwamnan Jihar Abiya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Farfesa Uche Ikonne ya riga mu gidan gaskiya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da dansa, Dokta Uche Ikonne ya fitar a wannan Larabar.

“Ina mai bakin cikin sanar da rasuwar mahaifina, Farfesa Eleazer Uchenna Ikonne.

“Ya rasu bayan ’yar takaitacciyar jinya a Babban Asibitin Kasa da ke Abuja da misalin karfe 4 na Asubahin ranar 25 ga watan Janairun 2023.

“Ya fara samun sauki bayan jinyar da ya yi a Birtaniya, amma a kwanaki kadan da suka gabata sai ya kamu da bugun zuciya wanda hakan ne ya yi sanadiyar ajalinsa.

“Za a fitar da karin jawabi da zarar iyalansa sun yanke shawara game da batun jana’izarsa.”

Mutuwar dan takarar gwamnan dai na zuwa ne kimanin wata guda gabanin Babban Zabe na 2023.