✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar gwamnan PRP ya rasu mako 1 bayan kaddamarwa

Farfesa Bangbose ya rasu mako daya bayan ya zama dan takarar gwamnan Jam'iyyar PRP na Jihar Ogun

Dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PRP a Jihar Ogun, Farfesa David Bamgbose, ya rasu mako guda bayan jam’iyyar ta kaddamar da shi gabanin zaben 2023.

A ranar Juma’a ِAllah Ya karbi ran Farfesa Bamgbose, wanda Shugaban Jam’iyyar PRP na Jihar Ogun, Samson Ogunsanya ya kaddamar a ranar Asabar da ta gabata, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a Abeokuta.

Hadimin mamacin, Oduntan Olayemi, ya shaida wa Aminiya cewa Farfesa Bamgbose ya rasu ne a safiyar Juma’a a Asibitin Lantoro da ke a Abeokuta, babban birnin jihar, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Ya ce a ranar Alhamis aka kai Bamgbose wani asibiti da ke Olomore bayan ya nuna alamun gajiya a tattare shi, inda daga nan aka tura shi Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Abeokuta domin a yi masa gwaje-gwaje.

“Amma saboda tsananin halin da yake ciki, sai muka kai shi asibitin jiha da ke Lantoro, inda aka kwantar da shi a sashen jinya na gaggawa, aka sanya masa iskar oksijin (ranar Juma’a).

“Da safe da na je sai na samu naya numfashi da sauri kuma da karfi. Bayan na je sayo magungunan da aka rubuta, sai aka kira ni a waya cewa rai ya yi halinsa,” in ji Olayemi.

Mamacin, wanda limamin coci ne, ya rasu ya bar matarsa, Mary Bangbose da ‘ya’ya shi.

A baya mamacin ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya janye wa Ladi Adebutu, wandan ya zama takarar jam’iyyar.

A lokacin ficewar Farfesa Bamgbose daga PDP, ya bayyana rashin adalci da aka yi masa da rashin tafiya da mutane a jam’iyyar a matsayin dalilansa.