✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan takarar majalisar PDP a Kebbi ya rasu 

Dan takarar ya rasu bayan dawowa daga ziyartar mahaifinsa da ke jinya a Amurka ziyara.

Dan takarar Majalisar Tarayya a Jam’iyyar PDP a mazabar Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza, Abba Muhammed Bello, ya rasu.

Bello ya yi rasu ne bayan dawowa daga ziyartar mahaifinsa, Muhammed Haliru Bello wanda tsohon shugaban jam’iyyar PDP ne a Kebbi, da ke jinya a Amurka ziyara.

Dan takarar na PDP, ya lashe zaben fid-da-gwanin jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu.

Bello ya kayar da dan majalisar da ke ci a yanzu, Alhaji Mohammed Bello Yakubu wanda hakan ya sa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a bayyana musabbabin rasuwar dan takarar na PDP ba.