✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar Sanatan APC a Jigawa ya riga mu gidan gaskiya

Gwamna Badaru ya jajanta wa iyalan mamacin.

Dan takarar Sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma a jam’iyyar APC, Tijjani Ibrahim Kiyawa, ya riga mu gidan gaskiya.

Tijjaniya Kiyawa ra rasu ne ranar Asabar a wani asibiti a kasar Sin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ciwon huhu ne ya sanya aka soma kwantar da shi ne a wani asibiti a Abuja, babban birnin Najeriya.

Sai dai daga bisani an garzaya da shi kasar China domin ci gaba da kula da lafiyarsa bayan yanayin jikinsa ya kara tabarbarewa.

Watanni uku da suka gabata ne Marigayi Kiyawa ya lashe tikitin takarar Sanata na jami’yyar APC na mazabar Kudu maso Yammacin Jigawa.

Gwamna Muhammad Badaru, ya bayyana rasuwar Kiyawa a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, hatta ga al’ummar musulmi baki daya.

A wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Habibu Nuhu Kila, ya jajanta wa iyalan mamacin.

“Ya bayyana marigayi Alhaji Tijjani Ibrahim Kiyawa a matsayin dan siyasa mai kishin kasa kuma mai rikon amana wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban siyasar kasar nan.

“Gwamna Badaru ya roki Allah Madaukakin Sarki Ya sa mutuwa ta zamo hutu a gareshi, tare bai wa iyalansa hakurin jure rashin da suka yi,” in ji sanarwar.

Marigayin ya taba wakiltar mazabar Dutse/Kiyawa a Majalisar Wakilai tsakanin 2011 zuwa 2015.