✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar Shugaban Kasa na ADC ya kamu da Coronavirus 

Kar mu bari siyasa ta mayar mana da hannun agogo baya wajen yakar cutar.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya kamu da Coronavirus bayan sakamakon gwaji ya tabbatar yana dauke da kwayoyin cutar.

Mista Kachikwu ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya fitar a ranar Asabar, yana mai gargadin ’yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan don annobar na iya dawowa.

Ya bayyana cewa tuni ya killace kansa kuma ya daina halartar tarukan jama’a da duk wasu harkalloli da suka danganci cudanya da al’umma.

Dan takarar ya ja hankalin ’yan Najeriya a kan kada su kuskura su yi wa cutar Coronavirus rikon sakainar kashi.

Ya ce a halin yanzu alkaluman masu kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa cikin makonnin baya–bayan nan ko’ina a fadin duniya.

“Bai kamata ’yan Najeriya su yi kasa a gwiwa ba duk da cewa gwamnati ta sassauta dokokin COVID-19.

“Tsare-tsare da kuma tanadin da gwamnati ta yi a fannin kiwon lafiyarmu ba zai haifar da da mai ido ba a yayin da wannan annoba ke neman sake barkewa musamman a daidai lokacin da kwararrun masu kula da harkokin kiwon lafiyar ke tururuwar barin kasar.

“Dole ne mu kara kaimi wajen yi wa al’umma gwaje-gwaje da daukar duk matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.

“Kada mu zuba ido yawon yakin neman zabe da sauran tarukan siyasa su zama silar yaduwar COVID-19.

“Kar mu bari siyasa ta mayar mana da hannun agogo baya a nasarorin da aka samu wajen yakar cutar.

“Za mu tsira daga cutar Coronavirus idan kowannenmu zai kasance mai lura da sa ido sosai,” in ji Kachikwu.