✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan uwan Sarkin Musulmi ya rasu

Wan Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya rasu

Allah Ya yi wa yayan Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III rasuwa.

Alhaji Buhari Abubakar III ya rasu ne ranar Juma’a a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, bayan fama da rashin lafiya.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Buhari Abubakar III shi ne Hakimin Sakkwato ta Arewa.

Rasuwar tasa ita ce babba ta biyu da aka yi a gidan sarautar Masarautar Daular Usmaniyya a rana guda.

Tun da farko Aminiya ta kawo rahoton rasuwar ’yar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello, mai suna Aisha.

Sardauna Ahmadu Bello, jika ne ga Sarki Muhammadu Bello, wanda da ne ga Shehu Usmanu Danfodiyo, wanda ya assasa Daular ta Usmaniyya.

Hajiya A’i, kamar yadda aka fi sanin ta, ta rasu tana da shekara 76, a asibiti a birnin Dubai na Haddaddiyar Daular Larabawa, inda aka yi  jinyar ta, Hassan Dambaba, ya sanar.

Marigayiyar, ita ce ta biyu a cikin ’ya’yan marigayi Sardauna, kuma mata  ce ga marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmad Danbaba.