✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote bai kara farashin sukari ba —Sambajo

Alhaji Salisu Sambajo ya ce ’yan kasuwa ne ke kara farashi ba kamfanin Dangote ba

Daya daga cikin manyan ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Salisu Sambajo ya ce har yanzu kamfanin Dangote bai kara farashin sukari ba.

Sambajo, wanda babban dilan Dangote ne, ya kara da cewa Dangote bai taba kara farashin sukari ba a watan Ramadan, yadda ake ta rade-radi.

“Ko kwabo ba a kara ba kuma ba su rage ba. Abin da aka yi shi ne N18,500, saboda haka mu abin da muke sayar da sukari a nan N18,300.

“Ko yanzu idan da akwai mai bukata, ya zo ni zan ba shi mota 10 a suto dina. In kuma yana so ya kara zan kai shi suto din Dangote, ya biya mota 100 a dora masa, duk inda zai kai ya kai,” a cewarsa.

Game da zargin kara farashin sukari da ake zargin kamfanin da yi a watan Ramadan —lokacin da aka fi bukatarsa— Alhaji Salisu Sambajo ya ce ’yan kasuwa ne ke kara farashi, amma kamfanin bai taba yin haka ba.

“Babu wani watan azumi da ya zo Dangote ya kara kudin sukari. Sai dai a zo a kara a nan cikin kasuwa,” inji shi.

Ya bayyana cewa kamfanin ba shi da ikon kayyade wa ’yan kasuwa na cikin unguwanni ko kauyuka farashin da za su sayar, saboda kowannensu da irin dawainiyar da yake yi kafin ya kai kayan wurin da zai rika sayarwa.

“Mutum ne ya zo tun daga unguwarsu ya sayi sukari buhu daya a hannunka, ya sa a a-kori-kura, ya kai unguwarsu yana sayarwa, wannan kana da iko da shi?

“Kamar mutum ne ya zo daga kauye ya sayi kaya a wurinmu. Ko mota 20 ya saya, mu dai ga abin da muka ba shi. To kuma ya danganta nawa zai sayar a garinsu. Za mu bi shi can ne mu ce masa ga yadda zai sayar? Wannan ai ya fi karfin aikinmu,” inji Alhaji Sambajo.