✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dangote da BUA ke da izinin kawo sukari daga waje’

CBN ya hana ba wa daukacin masu shigo da sukari daga waje canjin Dala

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu kamfanonin Dangote da BUA da kuma Golden Sugar ne kadai ke da izinin shigo da sukari daga kasashe waje.

Daraktan Kasuwanci da Canjin Kudi na CBN, O.S. Nnaji ya ce CBN ya ba da lasisi ga kamfanonin uku wadanda kowannensu ya mallaki masana’antar sarrafa sukari, domin shigo da ita Najeriya.

Sanarwar tasa ta ce CBN ta kuma hana ba da canjin Dala ga ’yan kasuwa masu shigo da sukari face kamfanonin na Dangote da BUA da kuma Golden — su ma din sai sun samu sahalewar CBN.

Babban Bankin ya ce ya yi hakan ne lura da kokarin kamfanoin wajen karkato da akalar harkokinsu zuwa cikin gida da zummar bunkasa bangaren.

Nnaji ya ce kamfanonin sun yi rawar gani a bangaren bunkasa harkar sarrafa sukari a cikin gida, wanda ya zo daidai da manufar Gwamnatin.

Shirin bunkasa harkar sarrafa sukari a cikin gida na gwamnati ya dora wa CBN alhakin lura da yadda ’yan kasuwa ke karkato da akalar masana’antunsu domin samar da wadatacciyar sukari a cikin gida.