✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote da BUA za su gina tituna masu tsawon kilomita 794

Jihohi 11 za su amfana da aikin gina manyan hanyoyin.

Kamfanonin Dangote da BUA da kuma kamfanin sadarwa na MTN za su gina gadoji da manyan tituna masu tsawon kilimota 794 a Najeriya da kudin harajin da ya kamata su ba wa gwamnati.

Ministan Sadarwa, Lai Mohammed ya ce jihohi 11 daga yankunan siyasa shida da ke Najeriya ne za su amfana da manyan tituna da gadoji da kamfanoni za su gina wa Gwamnatin a karkashin tsarinta na Gidanawa da kuma Gyaran Tituna da Bashin Kudin Haraji.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta riga ta ware wasu manyan hanyoyi da gadoji da ta ba wa muhimmanci domin kamfanoni su gina da kudin harajinsu.

Lai Mohammed ya ce tuni Kamfanin Masan’antun Dangote da BUA da MTN suka rungumi tsarin, inda za su gina wa gwamnati manyan hanyoyi da gadoji a madadin kudin harajin da za su biya ta.

Sauran kamfanonin su ne kamfanin gine-gine na Julius Berger da Unilever da Bankin Access da Transcorp da Lafarge da kuma Kamfanin Masana’antun GZI.

A karkashin tsarin ne aka gina hanyoyi da bashin kudin haraji ne aka gina titin kankare mafi tsawo a Najeriya, daga Obajana zuwa Kabba a Jihar Kogi, wanda tsawonsa ya kai kilomita 43.

Mista Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ta gina manyan hanyoyin akalla 28 a fadin Najeriya da tsarin rance na Sukuk.

Ya jaddada amfanin kasashen yammacin duniya su fahimci muhimmancin taimaka wa kasashe masu tasowa irin Najeriya a bangaren samar da ababen more rayuwa.

Ta hakan ne, a cewar, kasashen za su samar da ayyukan yi, musamman ga matasa, wadanda idan suka samu abin yi, miyagun kungiyoyi irin Boko Haram ba za su iya yaudarar su ba.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga kafafen labarai kwararru da masu fada a ji na duniya  birnin Washington na kasar Amurka, Lai Mohammed.

An shirya taron ne domin fahimtar da mahalarta irin abuwan da ke wakana a Najeriya a bangaren nasarorin da ta samu da kuma matsalolin da suka yi mata tarnake.

Ministan ya shaida wa taron cewa Najeriya ta bayar da muhimmanci ga batun hadin gwiga da kuma taimakon kasashe domin bunkasa bangaren samar da wutar lantarki.

“Mun kaddamar da babban aiki na samar da karin wutar lantarki mai karfin megawatta 3,000 daga Tashar Lantarki ta Mambilla wadda zai ci Dala biliyan 5.8.

“Mun samu rancen kudi daga kasar China, wadda za ta dauki nauyin kashi 85 cikin 100 na aikin, mu kuma za mu samar da ragowar kashi 15 na abin da za a kashe.

“Idan aka kammala, aikin zai bude sabon babi a bangaren samar da wutar lantarki a Najeriya,’’ inji shi.