✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dantata ya dauki nauyin karatun mutum 100 a sabuwar Jami’ar Al-Istiqama

Dukkansu za su kasance 'ya'yan talakawa don a taimaka musu wajen gina rayuwa.

Shaharraren attajiri kuma fitaccen dan kasuwa a Kano, Alhaji Dokta Aminu Alhassan Dantata, ya dauki nauyin dalibai guda 100 da za su yi karatu kyauta a sabuwar jami’ar Al-Istiqama da ke garin Sumaila a Jihar Kano.

Daliban za su yi karatu kyauta a karkashin tsarin bayar da tallafin karatu na Alhaji Aminu Dantata da ya saba daukar nauyi.

Dantata ya bayyana cewa, a cikin irin gudunmawar da yake bai wa harkar ilimi, ya dauki nauyin dalibai guda dari kuma dukkansu za su kasance ‘ya’yan talakawa don a taimaka musu su gina rayuwarsu.

Dantata ya yi godiya ga Allah da ya sanya aka zabi Farfesa Salisu Shehu a matsayin shugaban sabuwar jami’ar na farko, a cewarsa, “Farfesa Shehu mutumin kirki ne mai kula da addini da kuma taka tsantsan.”

A nasa jawabin a madadin kwamitin gudanarwa na jami’ar, Honarabul Kawu Sumaila ya yi addu’a kan Allah ya yalwata masa arzikinsa, ya kuma saka masa da alheri, ya tsawaita rayuwarsa cikin yalwar arziki da wadata da koshin lafiya.

Ana iya tuna cewa shekaru biyu da suka gabata ne tsohon wakilin Majalisar Wakilar ta Tarayya wanda ya wakilci Kananan Hukumomin Takai da Sumaila na Kano, Honarabul Kawu Sumaila, ya kafa sabuwar jami’ar Al-Istikama  a garin Sumaila.

Lamarin haka ya sanya Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jinjina wa tsohon mashawarci na musamman kan harkokin Majalisa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa kawo wannan gagarumin aikin jihar Kano, musamman a wannan lokaci da ake bukatar inganta harkokin ilimi.