✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darajar kudin Rasha ta fadi

An soma ganin tasirin takunkuman da Amurka da kasashen Tarayyar Turai suka kakaba wa Rasha.

Rahotanni sun bayyana cewa, darajar kudin Rasha na Ruble a kasuwannin nahiyar Asiya ta fadi da kashi uku bisa hudu.

Wannan dai ya nuna cewa an soma ganin tasirin takunkuman da Amurka da kasashen Tarayyar Turai suka kakaba wa Rasha don ganin tattalin arzikinta ya tabarbare biyo bayan mamayar da dakarun sojinta suka yi wa kasar Ukraine.

Haka kuma bayanai sun ce farashin danyen mai ya yi sama da kusan kashi hudu cikin 100.

Kudin Ruble na Rasha ya dai fadi da kusan kashi 41 cikin dari idan aka kwatanta da dala a ranar Litinin, bayan da kasashen Yammacin duniya suka kaddamar da wani gagarumin takunkumi a ranar Asabar, ciki har da hana wasu bankunan kasar Rasha amfai da tsarin biyan kudi na SWIFT na kasa da kasa.

Tuni dai ta fara daukar mataki inda Babban Bankin Rasha ya bayar da umarnin dakatar da tallata hannayen jarin kasashen waje da kuma wadanda ke son sayar da hannun jarinsu na Rasha.

Hukumomi a Tarayyar Turai sun ce wasu kamfanoni mallakar Rasha da ke cikin kasashensu musamman Sberbank wanda banki ne mallakar Rasha na daf da samun karayar arziki.

Babban Bankin Tarayyar Turai ya ce Sberbank wanda yake a Croatia da Slovenia ya shiga mawuyacin hali sakamakon yadda jama’a suka yi ta zare kudadensu.

Tuni ’yan kasar Rasha ke bin dogayen layuka sakamakon fargabar da suke yi na cewa katin bankinsu zai daina aiki kuma za a iya kayyade adadin kudin da mutum zai iya cira daga banki.