Daily Trust Aminiya - Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (2)
Subscribe

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (2)

Bayan ya girma ne sai suka sanya shi a makarantar sakandare.

Sai dai ba a dade ba sai suka yanke shawarar mayar da Ibrahim makarantar sakandare ta kwana domin a ganinsu hakan zai sa ya samu isasshen ilimi ba tare da hulda da abokan da watakila za su iya hana shi yin karatu a gida ba.

Bayan an mayar da Ibrahim makarantar sakandare ta kwana, sai ya ci gaba da karatunsa ba tare da wata matsala ba. Sai dai mahaifinsa Malam Usman yakan kai masa ziyara daga lokaci zuwa lokaci, sannan ya sanya wadansu daga cikin shugabannin makarantar su rika sanya ido a kan Ibrahim kuma idan yana bukatar wani abu ya rika tuntubarsu.

Ibrahim yaro ne mai biyayya da jin maganar iyayensa. Hasali ma ba ya so ya ga ya aikata wani abu da zai bata musu rai, don haka a kullum yake taka-tsantsan yayin da iyayen nasa suke sanya masa albarka.

Kwanci-tashi har Ibrahim ya kai shekarar karshe a karatun da yake yi. Bayan ya kammala sai ya samu kyakkyawan sakamako wanda hakan ya sa bai bata lokaci a gida ba ya samu wucewa jami’a don ci gaba da karatu.  Sai dai jami’ar da ya tafi karatu ba a garinsu take ba, ma’ana ya dan yi nisa da gida. Da yake ya riga ya zama saurayi kuma ya samu kyakkyawar tarbiyya Malam Usman, mahaifinsa da Hajiya Delu mahaifiyarsa ba su da wata ja a kan Ibrahim, don sun tabbatar duk inda dansu ya tsinci kansa, zai rike kansa ba tare da wata matsala ba. Sai dai a kowane lokaci sukan yi masa fada kan ya rike gaskiya da amana da kuma yin ibada a kan lokaci. Kada ya rika biye wa abokan da ba su da tarbiyya musamman wadanda ba su damu da yin karatu ko ibada ba.

Da yake Ibrahim yana karatun banagaren likita ne, ya kasance yana daya daga cikin daliban da suka fi nuna kwazo wanda hakan ya sa ya yi suna a tsakanin ’yan uwansa dalibai da malamai da mahukunta makarantar.

Sannu a hankali karatun Ibrahim ya yi nisa har ya kai mataki na karshe. Bayan ya kammala ne sai aka tura shi hidimar kasa a wata jiha.

Sai dai a lokacin da Ibrahim yake ajin karshe sun shaku da wata  budurwa da ita ma ajinsu daya mai suna Samira.  Yarinya ce mai ladabi da biyayya kuma ga kokari.  Saboda shakuwar da suka yi da Ibrahim a makaranta ya sa hatta abokansa suke musu lakabi da cingam. A kowane lokaci za ka same su tare ko dai suna yin karatu ta hanyar fadakar da juna ko kuma ziyartar dakin cin abinci tare.

Daga nan ne suka yi wa juna alkawarin insha Allahu za su auri juna da zarar sun kammala hidimar kasa kuma sun samu aiki.

Mu kwana nan

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805

More Stories