Daily Trust Aminiya - Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (3)
Subscribe

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (3)

Kodayake ba garin Ibrahim da Samira daya ba, makaranta ce kawai ta hadu su amma suna makwabtakar juna ne.  An tura su hidimar kasa ne a garuruwa daban-daban da hakan ta sa sai ta waya kawai suke tuntubar juna.

A gida kuwa ashe mahaifan Ibrahim sun zabar masa wata ’yar uwarsa mai hankali mai suna Halima da nufin hada su aure.  Auren zumunci ne kuma yarinya ce mai natsuwa da ladabi da biyayya.  Don haka mahaifin Ibrahim Malam Usman ya shawarci matarsa Delu a kan su daura wa Ibrahim aure da Halima sannan ta tare ba tare da saninsa ba.  Ita dai Halima ba ta yi karatun boko mai zurfi ba.  A matakin sakandare kawai ta tsaya.

Malam Usman ya ce saboda amincewar da ya yi wa Ibrahim ya tabbatar ba zai ba shi kunya  game da wannan aure ba, kuma zai amince ya karbe ta da hannu bibbiyu.

Malam Usman sai ya kira abokin Ibrahim wanda suka taso tun suna yara mai suna Musa, ya shaida masa abin da suka yanke  game da auren Ibrahim. Musa ya ce shi zai wakilci Ibrahim, inda za a yi shagalin bikin ba tare da sanin Ibrahim ba. Malam Usman ya gargadi Musa da kada ya kuskura ya sanar da Ibrahim halin da ake ciki har sai ya gama hidimar kasa ya koma gida.  Malam Usman ya shaida wa Musa cewa ya yi wannan dabara ce don kada a raba wa Ibrahim hankali biyu, domin muddin ya samu labarin an yi masa aure hankalinsa zai rabu biyu musamman a kan hidimar kasar da yake yi.

Malam Usman ya biya sadakin Halima a madadin dansa Ibrahim inda aka sha shagali.  Ya sa aka gyara dakin Ibrahim sannan amarya ta tare tana jiran dawowar angonta.

Duk abin da ake yi Ibrahim bai sani ba, kuma babu wanda ya fada masa ko ta waya.

Bayan Ibrahim ya kare hidimar kasa ne sai ya koma gida. Yana murna ya kammala hidimar kasa kuma abin da ya rage masa shi ne ya fara neman aiki don ya fara shirin auren Samira, amma kafin nan ya yanke shawarar zai sanar da mahaifansa game da masoyiyarsa Samira.

Bai san kaddara ta riga fata ba, tuni aka daura masa aure da Halima kuma har ta tare a dakinsa da ke cikin gidansu.

Mu kwana nan

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805

More Stories