✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darasin Haduwar Buhari da Obasanjo a Habasha

A ko da yaushe hankulan shugabannin kasashen duniya na kan Najeriya a matsayinta na babbar kasar bakaken fata da ke bin tafarkin dimokuradiyya  a duniya,…

A ko da yaushe hankulan shugabannin kasashen duniya na kan Najeriya a matsayinta na babbar kasar bakaken fata da ke bin tafarkin dimokuradiyya  a duniya, musamman  don su fahimci irin rawar da shugabanninta ke takawa wajen inganta harkokin siyasa da na  zamantakewa da kuma mulki.  Suna sane da dukkan irin rawar da ake takawa a kasar, sun kuma san irin takun-sakar da ta wanzu tsakanin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da Malam Muhammadu Buhari wanda ke bisa karagar mulki dangane da zaben shugabancin kasa da za a yi a farkon shekara mai zuwa. Suna sane da wata zungureriyar wasikar da Obasanjo ya rubuta wa shugaban kasa da kuma irin martanin da aka mayar mar.

To, ko da Shugaba Buhari da  Obasanjo suka hadu a wajen taron ka’ida na shugabannin kungiyar hada kan kasashen Afirka  sukan yi shekara-shekara a  birnin Addis Ababa na kasar Habasha (Ethopia) a karshen makon jiya  ba su yi  mamakin ganin yadda suka mance da cewa akwai wata takaddama da ta hada su, suka kuma  rungumi juna, sa’annan suka yi musabaha mai armashi, wacce ta burge kowa. Sa’ilin da suka sadu, har suna ta  barkwanci da juna  cikin raha da annashiwa, akwai wani tsohon shugaban kasa, Janar Abdussalami Abubakar, wanda shi da wasu suka yi ta  kyakyata dariya saboda  zantuttukan da suka  biyo bayan ganawar shugabannin biyu. Ko da akwai wata hiyana da nunkufurci a zukatansu ba su bayyana shi ba a fili, sun nuna cewa ba domin tuwo aka yi ciki  ba, ana iya amfani da shi domin hadiye bakar magana ko wani bacin rai.

Wannan shi ake kira dattaku da sanin ya kamata domin kuwa shugabannin biyu sun nuna cewa  su ne bijiman Najeriya, kasar da ake mata lakabi da  Giwar Afirka. Irin wannan dabi’ar ce shugabannin jamhuriyar farko suka a yi ta nunawa a nan cikin gida idan sun bayyana a gaban jama’a duk kuwa da cewa akwai bakar adawar da ke janyo rashin jituwa da tashin-tashina tsakanin magoya bayansu. A waccan lokacin ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta NEPU a Arewa  sun gamu da taskun da ba ta misaltuwa a hannayen sarakunan gargajiya masu goyon bayan jam’iyyar NPC mai mulki wadanda suka yi ta daddaure su kamar huhun goro. Amma duk da haka nan wannan al’amari bai gurbata dangantaka tsakanin shugaban jam’iyyar NPC, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da na jam’iyyar NEPU, Malam Aminu Kano ba.  A duk inda suka hadu za su yi kyakkyawar gaisuwa su kuma rungumi juna, su nuna tamkar babatu wata jayayya ko damuwa a dangantakarsu. Abin da suke nuna wa magoya bayansu dangane da haka shi ne kishin Arewacin Najeriya, wacce suke fatan ganin ta kamo takwarorinta na kudanci har ma ta dara su.  Idan kuma suka tashi yin sallamar rabuwa da juna Sardauna zai raka Malam Aminu har bakin motarsa, ya kuma ce da shi kada su bari a gane, shi kuwa Malam Aminu zai amsa da cewa ai ba za su gane ba.

Irin wannan fahimta da hada kai ne tsakanin Aminu Kano da Sardauna ta kai Malam Aminu Kano gwale ‘yan jam’iyyar NEPU wadanda suka firfito bisa kan titunan birnin Kano, hululu dauke da tsintsiya  don su share abin da suka kira bakin mulkin Sardauna da jam’iyyar NPC. Sa’ilin da suka iso kofar gidan Malam Aminu, ya kuma fito don ya yi musu jawabi, sai ya ce da su ba murna za su yi don an kashe wanda suke adawa da shi ba, domin kuwa murnarsu za ta koma ciki, kuma nan gaba za su yi kukan rashinsa saboda abubuwan da yake kare musu. Haka nan kuma a Jamhuriya ta biyu an yi bakar siyasar da ta haddasa matsananciyar gaba tsakanin Shugaba Shehu Shagari na jam’iyyar NPN  da kuma madugun adawar jam’iyyar UPN, Cif Obafemi Awolowo, amma duk da haka nan akwai hadin kai da fahimtar juna tsakaninsu, ba su kuma bari bangon Najeriya ya tsage ba, ta yadda kadangarun bariki za su ji dadin kurdawa don su bata ruwa.

Ko a wancan lokacin ma an yi mummunar gaba tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar PRP  wacce ta mulki Jihar Kano, inda bayan darewarta gida biyu Gwamna Muhammad Abubakar Rimi da kuma Sanata Sabo Bakin Zuwo  kowsannensu ya ja bangare guda. Duk da cewa an kasa sasanta tsakaninsu har hakan ya yi sanadiyyar rikice-rikice da tashen-tashen hankula da zubar da jini, sakamakon haka  bai yi wa gwamnan da ke mulki, Abubakar Rimi  kyau ba domin kuwa yana ji yana gani abokin adawarsa ya buga shi da kasa a zaben `1983. To amma me ya faru daga bisani? Ai haduwa suka yi a kurkukun Benin, inda Shugaba Muhammadu Buhari, sa’ilin yana sanye da khaki, ya daddare su. Wannan yanayin da suka samu kawunansu a ciki ya tilasta musu sasantawa da gafarta wa juna, kuma bayan fitowarsu daga jarun sai suka koma suka hade tamkar ba su ba, magoya bayansu kuma suka mayar da wukadensu kube. 

To, a yanzu ga tarihi can na maimaita  irin wancan mummunar lamarin da ya wakana tsakanin Gwamna Rimi da Sanata Bakin Zuwo, inda tsohon Gwamna, Sanata Rabi’u Musa Kwankwasi da kuma gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje suka tsaga jam’iyyar da ke mulkin jihar, APC gida biyu, kuma ko wanne bangare bai jituwa da dayan sai yawan fada kamar kaji.  Kai, har ma ta kai babu wata igiyar dangantaka wacce ba a tsinka ta ba, sa’annan a sakamakon haka babu irin badakalar da ta wanzu a jihar a zamanin mulkin jam’iyyar PRP, wacce ba a  koma takanta  ba.  Rahotanni na cewa bangaren Sanata Kwamkwaso, watau Kwankwasiyya sun dukufa ka’in da na’in wajen hambarar da gwamnatin daya bangaren na Gandujiyya don su dora nasu wanda zai yi biyayya ga manufofi da akidojin Kwankwasiyya. 

To babban abin da ake ji wa tsoro game da wannan al’amari mai ban takaici shi ne jam’iyyar APC na iya yin asarar kujerar gwamna a zabe mai zuwa ga tsohon gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau, wanda ke alkinta jam’iyyar PDP don ta dauko  fansa. Haka nan kuma ana fargabar cewa jam’iyyar APC na iya asarar fiye da rabin miliyoyin kuri’un Jihar Kano a zabe mai zuwa muddin ba an sasanta Kwankwasiyya da Gandujiyya ne ba. A shiyyar Arewa maso-Yamma, wacce ta fi sauran shiyyoyin yawan kuri’u  Jihar Kano ce babbar giwa, ita ce kuma sauran jihohin shiyyar ke kwaikwaya a harkokin siyasa, saboda haka nan idan ta yi atishawa sauran jihohin Arewa kafataninsu za su tashi da mura. Saboda haka sai jam’iyyar APC ta yi hattara don kada a haifi dan da ba idanu a zaben shugaban kasa mai zuwa.