✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daruruwan rumfunan katako sun kone a kasuwar Laranto a Jos

Gobara ta cinye daruruwan rumfunan a Kasuwar Katako da ke garin Jos, Jihar Filato daren Talata. Wutar ta tashi ne a layin masu katako na…

Gobara ta cinye daruruwan rumfunan a Kasuwar Katako da ke garin Jos, Jihar Filato daren Talata.

Wutar ta tashi ne a layin masu katako na Timber ‘B’ Hausa a kasuwar da ke unguwar Laranto, Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Kusan shekara 10 ke nan gobara na tashi a kasuwar duk shekara musamman da hunturu a watannin Nuwamba zuwa Disamba.

Shugaban ’yan kasuwar a layin, Alhaji Yusuf Aliyu Umar ya ce ba a san musabbabin gobarar ba wadda tashi wuraren karfe 11 na dare kuma ta yi fiye da sa’a biyu tana ci.

Wani bangare na kasuwar da gobarar ta cinye
Abin da ya yi saura daga sashen kasuwar da gobarar ta cinye.

Alhaji Yusuf ya ce ’yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe wutar amma kafin su zo ta riga ta riga ta cinye dukiya ta miliyoyin Naira.

Ya koka cewa shekara da shekaru suna rokon gwamnati ta samar da kayan kashe gobara a duk sadda bukata ta taso amma ba ta yi ba.

Wasu mutane da duba irin barnar da gobarar ta daren Talata ta yi a kasuwar.

“Saboda yawan samun gobara a kasuwar mun yi ta rokon ta samar da motar kashe gobara a kasuwar ko ta haka rijiyar burtsatse da za ta taimaka idan bukata ta taso amma shiru kake ji.

“Muna kara rokon gwamnati ta kawo mana dauki; ba kudi muka ce ta ba mu ba, kayan amfani a lokacin gaggawa muke bukata”, inji shi.