✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (7)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, za mu ci gaba da wannan labari…

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan makon, za mu ci gaba da wannan labari mai dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantatta kuma mai nasara. Ga ci gaba daga inda muka tsaya:

“Da zarar gari ya waye, ka samu kanka a raye, abu na farko da za ka yi shi ne, ka yi godiya ga Allah, sannan ka kuduri aniyar cin gajiyar dukkan lokacinka na yau. Idan kana da iyali, yi kokari ka fita hakkinsu a yau din nan. Duk nauyinsu da ke kanka a yau, yi kokari ka sauke shi. Haka ma iyayenka, idan suna raye, sanya su cikin tunaninka, wato ka yi kokarin sauke nauyinsu da ke kanka. Haka su ma danginka na jini da makwabtanka na gida, suna da wani hakki a wajenka, yi kokarin ka sauke wannan nauyin a yau din nan. Idan ka fita wajen aiki ko kuma kasuwa wajen sana’arka, babban abin da za ka yi a yau din nan shi ne, yi kokari ka fita hakkin ma’aikatarka, ta wajen gudanar da aikinka cikin gaskiya da adalci daidai iyawarka. Ka rayu cikin ingantattar dangantaka tsakaninka da abokan aikinka. Idan kuma kai dan kasuwa ne, to da zarar ka fita shagonka, yi kokari ka gudanar da sana’arka cikin gaskiya da adalci. Ka kyautata dangantakarka da abokan cinikayyarka. Haka su ma makwabtanka na kasuwa, ka rayu a yau din nan cikin kyakkyawar zamantakewa tsakaninka da su.”

“Kana saurare na sosai?” Tambayar da Malam Baba ya yi wa Baban Larai ke nan.

Shi kuwa ya amsa da cewa: “Kwarai kuwa, ina saurarenka, kuma yanzu ne na kara fahimtar inda ka dosa.”

“Na’am. To ka kara ara mani kunnuwanka, ga wata ’yar tambaya da zan yi maka. Ka duba irin dimbin aikin da ke gabanka a yau kadai. Shin kana da lokacin da za ka bata wajen yin fushi ko yin mugunta ga wani? Na tabbata ba ka da wani isasshen lokacin da za ka bata wajen yin haka. A yau din nan, idan ka rayu cikin al’umma cikin kyautata dangantaka tsakaninka da rukunnan mutanen da na lissafa maka a baya, to tabbas za ka samu kanka cikin annashuwa da farin ciki. Lokacin da ka fita hakkin iyalanka da iyayenka da dangankinka da abokan aikinka ko sana’arka da sauran duk wanda za ka hadu da shi a yau, ina tabbatar maka da cewa ka ci ribar rayuwar yau din nan ke nan.”

“Don haka, sake sanya darasinmu na daya a ranka, ka wayi gari kullum kana tuna shi: Ka tattara dukkan al’amuranka, ka rayu a yau kadai. Sai kuma ka saurari darasi na biyu, cikin ukun da na ce zan shaida maka.

 

Za mu ci gaba