✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattijon da ke kwacen babur a Jigawa ya shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan Jigawa, ta kama wani tsoho mai shekaru 50 da ke kwacen baburan mutane a jihar. Kakakin rundunar jihar DSP Lawan Shiisu ne…

Rundunar ‘yan sandan Jigawa, ta kama wani tsoho mai shekaru 50 da ke kwacen baburan mutane a jihar.

Kakakin rundunar jihar DSP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Laraba a birnin Dutse.

“Ranar Juma’a ne muka samu kiran gaggawa daga wata majiya da kuma ‘yan bijilantin kauyen Shamarwa da ke Karamar Hukumar Auyo, cewa an kamo wani mutum mai shekaru 50 dan kauyen Musari da ke satar baburan mutane.

“Lokacin da aka kamo shi an same shi da babur samfurin Hagoue da injin ruwa da ya sato”, in ji Kakakin.

Shiisu ya kuma ce mazauna kauyen sun tabbatar da shi ne ke tare su a hanya yana yi musu kwacen babura, da satar musu kayayyaki da dama.