✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dauda Lawal na PDP ya kayar da Gwamnan Zamfara

Dauda Lawal wanda zabensa a matsayin dan takara ya zo da rudani ya kayar da Gwamna Matawalle

Dan takarar Jam’iyyar PDP, Dauda Lawal-Dare ya ci zaben Gwamnan Jihar Zamfara, inda ya kayar da gwamna mai ci, Bello Muhammad Matawalle da ke neman tazarce.

A wannan Talatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Dauda Lawal-Dare na ya zama zababben Gwamnan Jihar Zamfara bayan ya samu kuri’u 377,726 daga kananan hukumomi 14 da ke jihar.

Baturen zaben da aka gudanar ranar Asabar kuma Shugaban Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, Farfesa Kassimu Shehu, ya ce Gwamna mai ci Bello Matawalle na APC ne ya zo na biyu a zaben da kuri’u 311,976.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Matawalle ya ci zaben wa’adinsa na farko ne a Jam’iyyar PDP, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa APC mai mulki a matakin kasa.

Shi dai Dauda Lawal zaben sa a matsayin dan takarar PDP ya kasance mai cike da rudani, inda tun aka yi ta takaddama bayan da ya yi nasara a zaben farko.

Daga baya abokan takararsa suka je kotu, ta soke zaben, ta ba da umarnin a sake wani sabo, amma duk da haka ya sake yin nasara.

Aminiya ta ruwaito cewa kawo yanzu yana cikin jerin sabbin gwamnoni 14 da aka zaba a zaben gwamnonin da aka gudanar a jihohi 28 a Najeriya.

Ga jerin sunayensu, jihohinsu da kuma jihohin:

  1. Abba Kabir Yusuf (NNPP) — KANO
  2. Dikko Umar Radda (APC)  KATSINA
  3. Dauda Lawal Dare (PDP)  ZAMFARA
  4. Uba Sani (APC)  KADUNA
  5. Umar Namadi (APC) — JIGAWA
  6. Umaru Bago (APC)  NEJA
  7. Ahmad Aliyu (APC)  SAKKWATO
  8. Caleb Mutfwang (PDP)  FILATO
  9. Kefas Agbu (PDP)  TARABA
  10. Bassey Otu (APC)  KUROS RIBA
  11. Francis Nwifuru (APC)  EBONYI
  12. Sheriff Oborevwori (PDP)  DELTA
  13. Umo Eno (PDP)  AKWA IBOM 
  14. Hyacinth Alia (APC)  BINUWAI
  15. Siminialayi Fubara (PDP) — RIBAS.