✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daukar Aiki: Ranar Litinin za a saki sunayen mutanen da suka ci jarabawar Sibil Difens

Mutum 5,000 sun yi nasara daga cikin miliyan 1.5 da suka nemi aikin da aka fara dauka a 2019.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) za ta fitar da jerin sunayen mutum 5,000 da suka ci jarabawar daukar aikin da ta gudanar.

Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Abubakar Audi, ya ce za ta fitar da sunayensu daga ranar Litinin 17 ga watan Janairun da muke ciki.

Ya bayyana cewa daga ranar Litinin din mutanen da suka zana jarabwar za su iya duba sunayensu ta shafin hukumar, sannan za a fara tantance dakardun wadanda suka yi nasara a ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki, gabanin fara ba su horo.

Da take bayani, Sakatariyar Majalisar Daraktocin Hukumomin Sibil Difens, Kashe Gobara, Shige da Fice da Gidajen Yari, Aisha Rufai, ta ce, “Mutum 5,000 ne suka yi nasara. Yanzu matakin da muke ke nan. Kuma daga yau za mu fara  aikin tantance su.”

Ta kuma kore fargabar da ake yi na cewa za a soke batun daukar aikin da aka faro shi tun daga shekarar 2019.

Shugaban Hukumar, ya shaida wa manema Labarai a ranar Alhamis cewa tun a shekarar 2019 aka fada shirin daukar aikin, amma bullar cutar COVID-19 ta kawo masa tsaiko.

A cewarsa, ’yan Najeriya miliyan 1.5 suka nemi aikin da hukumar take da gurabun aiki 5,000.

“Daga baya a watan Maris na 2020 majalisar daraktocin hukumar ta bukaci su sabunta bayanansu, wanda mutum 217,00o suka amsa kira.

“Zuwa watan Disamban 2020 kuma mutum 53,116 daga cikinsu masu neman aikin suka sabunta takardunsu.

“Wannan adadin su ne wadanda aka kira suka rubuta jarabawar daukar aikin, ta intanet, wanda hukumar JAMB ta gudanar.
“Mutum, 6,500 ne suka kai matakin da za a tantance su domin daukar su aikin. Tun da aiki ne da aka faro, kuma yanzu an kammala, saura a fitar da sakamakon,” inji shi.
Sakatariyar Majalisar Daraktocin Hukumomin Sibil Difens, Kashe Gobara, Shige da Fice da Gidajen Yari, Aisha Rufai, ta ce, “An tantance takardun mutum 6,500 din kai-tsaye, daga ciki aka tabbatar da mutum 5,000 da za dauka aikin… Daga yau za mu fara  aikin tantance su,” kafin fara ba su horo.
Ta shawarci wadanda suka nemi aikin da su duba sunayensu a shafin daukar aikin hukumar da suka ziyarta a baya daga ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, 2022.