✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daya daga cikin Alhazan Neja ya rasu a Saudiyya

Hukumar jin dadin Alhazan Jihar ta tabbatar da rasuwar Alhajin.

Daya daga cikin Alhazan Najeriya daga Karamar Hukumar Wushishi ta jihar Neja, Alhaji Mamman Nasiru Zungeru, ya rasu a kasa mai tsarki.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Neja, Alhaji Umar Makun Lapai, ne ya sanar da hakan a kasar Saudiyya cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Hassan Idris, ya fitar a ranar Laraba.

Ya ce hukumomin kasar Saudiyya ne za su gudanar da jana’izarsa kamar yadda aka tanadar.

“Allah ya jikansa da rahama ya sa Aljanna Firdausi ce makoma a gare shi, ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashi da suka yi, Amin,” inji Shugaban hukumar Alhazan.

An samu mahajjata da dama daga Najeriya da kasashe da dama da suka rasu a kasa mai tsarki yayin Aikin Hajjin na Bana, wanda hukumomi suka danganta rasuwar tasu da ciwon zuciya ko kuma hawan jini da kuma sauran cututtuka.