✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daya daga cikin manyan sarakunan Oyo, Aseyin na Iseyin, ya rasu

Ya rasu yana da shekara 62 a duniya

Daya daga cikin manyan Sarakunan Jihar Oyo, mai martaba Aseyin na Iseyin, Oba Abdulganiyu Adekunle Salawudeen ya kwanta dama.

Marigayi basaraken mai shekaru 62 ya rasu ne a ranar Lahadi, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan da ke Ibadan bayan fama da rashin lafiya.

Tsohon likitan dabbobi, Aseyin na Iseyin, ya zama Sarki a masarautar Iseyin ne a shekarar 2007.

Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwar sa a ranar Lahadi.

Oba Abdulganiyu Adekunle Salawudeen dai yanzu ya shiga sahun manyan Sarakuna hudu da suka riga mu gidan gaskiya a Jihar Oyo da har yanzu ba a nada sababbin Sarakunan da za su gaji uku daga cikin su a masarautarsu ba.

Sarakunan da suka kwanta dama a baya-bayan nan a jihar sun hada da Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewunmi Ajagungbade da Alaafin na Oyo Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi da Asigangan na Igangan.