✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

D’banj: ‘Mu muka gayyaci ICPC kan badakalar N-Power’

Ma'aikatar Agaji da Ayyukan Jinkai ta ce ita ce ta gayyaci Hukumar ICPC kan zargin almundahanar kudaden shirin tallafin matasa na N-Power

Ma’aikatar Agaji da Ayyukan Jinkai ta ce ita ce ta gayyaci Hukumar Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC) kan zargin almundahanar kudaden shirin tallafin matasa na N-Power.

A ranar Laraba Aminiya ta kawo rahoton yadda Hukumar ICPC ta tsare fitaccen mawakin Najeriya, D’banj, kan zargin badakalar kudaden matasan N-Power.

Ma’aikatar ta ce, “Muna sane da cewa Hukumar ICPC ta gayyaci wadansu mutane domin su amsa tambayoyi kan badakalar.

“A yayin da hukumar ke gudanar da bincike, mun tsaurara matakan tsaro a kan shafukanmu domin dakile ayyukan bata-gari a nan gaba.”

Shirin tallafin wanda ke karkashin ma’aikatar, an tsara shi ne domin samar wa matasa musamman wadanda suka kammala karatu sana’o’i da kuma aikin wucin gadi.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin mawaki D’banj ne da hada baki da wasu jami’an shirin N-Power wajen yin cushen sunayen bogi a matsayin masu cin gajiyar shirin.

Ana kuma zargin cewa mawaki D’banj da jami’an gwamnatin ne ke karkatar da albashin matasan na bogi zuwa aljihunsu.

Ma’aikatar ta ce bayan wasu korafe-korafe da ta samu, ta gano cewa akwai wata kullalliya, shi ya sa ta bukaci Hukumar ICPC ta binciki lamarin.

Ta ce a halin yanzu tana aiki kafada-da-kafada da ICPC domin kammala binciken wannan badakalar.

Ma’aikatar ta kara da cewa domin tabbatar da yin komai a fili da kuma sa ido kan shirin N-Power da sauran shirye-shirye tallafin da ke karkashinta, ta yi hadin gwiwa da ICPC da hukumomin tsaro da kungiyoyin fararen hula domin tabbatar da komai na tafiya ba tare da cuwa-cuwa ba a duk jihohin Najeriya.