✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillalan mai sun dakatar da yajin aikin da suka shirya shiga ranar Talata

Tun da farko dai IPMAN ta shirya yakin aikin ne saboda rufe mata sakatariyar da aka yi.

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta dakatar da yajin aikin da ta kudiri aniyar farawa daga ranar Talata ta hanyar rufe dukkan gidajen man da ke kasar nan.

Sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Danladi Garba Pasali ne ya bayyana haka a yammacin Litinin.

Tun da farko dai IPMAN ta yi barazanar rufe dukkan gidajen man da ke Najeriya daga ranar Talata matukar Gwamnatin Tarayya da Babban Sufeto ’Yan Sandan ba su dauki mataki kan rufe sakatariyar kungiyar da jami’an ’yan sanda da ke Abuja suka yi ba.

Kungiyar dai na zargin cewar rufe mata sakatariyar da aka yi ranar Juma’a da cewa ba ya kan ka’ida.

Alhaji Danladi Garba Pasali ya ce sun ta dakatar da yajin aikin ne sakamakon zaman da suka yi da hukumar gudanarwar Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da wakilan Majalisar Tarayya da jami’an shaktwatar ’yan sanda ta kasa da kuma wakilan Fadar Shugaban Kasa a kan lamarin a ranar Litinin.

“Sakamakon abubuwan da muka tattauna da wadannan masu ruwa da tsakin, mun cimma matsaya kan ’yan kungiyarmu, su dakatar da wannan yajin aiki da muka tsara yi.

“Don haka, muna kira ga dukkan ’yan mambobinmu na shiyyoyi da jihohin kasar nan kan su dakatar da wannan yajin aiki da za ayi,” inji shi.