✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillalan man fetur a fadin Najeriya sun tsunduma yajin aiki

Kungiyar ta ce za matakin ya zama dole saboda asara kawai mambobinta ke tafkawa

Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta umarci mambobinta a fadin kasar nan da su tsunduma yajin aiki daga yanzu har sai abin da hali ya yi.

A sakamakon haka, kungiyar ta bukaci a rufe ilahirin gidajen man da ke kasar daga ranar Talata.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar na kasa, Mohammed Kuluwa, ya fitar ranar Talata.

IPMAN ta ce, “Sakamakon mawuyacin halin da muka tsinci kanmu a ciki wajen samo man da kuma sayar da shi da tsada, da kuma yadda hukumomi ke tilasta mana sayar da shi a kan farashin da muke faduwa.

“Muna umartar ilahirin mambobinmu da su dakatar da sayar da mai, sannan su dakatar da biyan kudin duk wani man da suka riga suke kokarin sarowa daga yanzu har sai abin da hali ya yi.”

Sanarwar ta dillalan man na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da dogayen layuka da wahalar man ta haifar a fadin kasar.

Kazalika, ana fama da tsadar man a kusan duk fadin kasar, inda a wasu wuraren ya haura N370 a kan kowacce lita, yayin da a wasu Jihohin kuma rahotanni suka ce har ma ya haura N400.

Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da karancin takardun kudi sakamakon canjin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.