✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillalan man fetur sun fara yajin aiki a jihohin Arewa

Akwai yiwuwar yajin aikin ya haifar da wahalar mai

Akwai yiwuwar a fuskanci wahalar man fetur a jihohin Arewacin Najeriya guda tara sakamakon tsunduma yajin aikin kwana uku da Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta fara.

Kungiyar ta fara yajin aikin ne a matsayin gargadi kan rashin biyansu kudaden da suke bi bashi da suka kai Naira biliyan 70.

Jihohi taran da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) yake da defot-defot sun hada da Borno da Adamawa da Kano da Kaduna da Binuwai da Filato da Gombe da Neja da kuma Sakkwato.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin a Maiduguri, babban birnim jihar Borno, kakakin kungiyar ta IPMAN a jihar, Abdulkadir Mustapha, ya ce rashin biyansu kudaden na jawo musu shan wahala,  inda ya ce, “Don haka mun yanke shawarar janye ayyukanmu da muke yi na kwana uku”.

Mustapha ya yi barazanar cewa, gazawar hukumomi wajen mayar da martani tare da biyan duk wasu kudaden da suke bin zai haifar da yajin aiki na dindindin da kuma rufe dukkanin gidajen man.

Ya ce, “Daga yanzu, duk kayayyakin da aka dage dole ne a daidaita su ko kuma a biya su a cikin wa’adin kwana 30 da aka kayyade kamar yadda aka amince a baya. Rashin yin hakan zai haifar da dakatar da ayyukanmu a dukkan gidajen man fetur da gidajen man da ke fadin Arewacin Najeriya.

“Kodayake, an biya wasu kudaden da ba su kai kashi biyar cikin 100 na bukatunmu ba, amma ba a daidaita yawancin kudaden da muke bi ba.

“Bugu da kari, kusan dukkan abin da muka ce muna bi na wannan shekara, da ma yawancin na shekarar 2019 zuwa 2021, har yanzu ba a biya su ba.

“Shekaru da dama muna ta bin diddigin yadda Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta ke yi, game da ikirarin da muka yi na na kudin da ba a biya ba wanda ya kai Naira biliyan 70 ba,” inji Shugaban na IPMAN.