✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dillan miyagun kwayoyi 48 sun fada komar NDLEA a Edo

An kama su ne a cikin wata daya a jihar

Akalla dillalan miyagun kwayoyi 48 ne suka fada a komar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA a watan Oktoba a Jihar Edo.

Haka nan, hukumar ta lalata gonaki guda 10 da ake zargin na tabar wiwi ne wanda girmansu ya kai kadada 8.23, tare da kama motoci uku da babur daya da ake amfani da su wajen sufurin miyagun kwayoyi jihar.

Kwamandan NDLEA na jihar, Mista Buba Wakawa ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) wadannan nasarori da suka samu ranar Litinin a Abuja.

Kazalika, Wakawa ya ce hukumar ta samu nasarar gurfanar da wadanda ta kama bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi da dama a cikin watan, kuma an yanke wa shida daga cikinsu hukunci daidai da laifin da suka aikata.

Daga cikin wadanda suka fada a komar hukumar dai akwai maza 39 da mata tara, inda aka kwace tabar wiwi da nauyinta ya kai kiligram 7,379.59, daga hannunsu.

(NAN)