✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dimokuradiyya a cikin jam’iyyu

Abu uku da ke iya faruwa tsakanin Ganduje da Shekarau bayan barakar da aka samu a APC.

A karshen makon jiya ne manyan jam’iyyun nan biyu, APC da PDP suka gudanar da zabubbukan shugabannin jam’iyyun a matakan jihohi.

Kusan kowace jiha an gudanar da irin wannan zabe, sai dai jihohin da suka yi nasu tuntuni.

A wasu jihohin ana ala-sam-barka, yayin da a wasu kuwa zabubbukan suka bar baya da kura, domin kuwa an samu sabani mai girman gaske da har ya kai wadansu suka gudanar da nasu zaben daban da suke ganin shi ne hanyar da za ta kai su ga tudun-mun-tsira.

Kasancewar mafiya yawanci an gudanar da zaben na bangaren PDP a wasu jihohin, inda aka yi zaben a ranar Asabar ba su da yawa, shi ya sa matsalolin da suka samu takaitattu ne kwarai.

Kuma kasancewar Jam’iyyar PDP tana adawa ce a yanzu, tirka-tirka da matsaloli sun yi karanci a jam’iyyar, duk da cewa ita ma akwai nata tarin matsaloli da rikicin cikin gida da kuma rarrabuwar kai, musamman a Kano da ake da bangarori biyu wato Kwankwasiyya da kuma bangaren su Aminu Wali.

Haka nan sauran jihohi da dama ake da irin wadannan gida-gida ko bangarori.

Sai dai kuma, irin wadannan matsaloli su ne abubuwan da suka dabaibaye Jam’iyyar APC mai mulki, watakila hakan yana da nasaba da cewa mutanen da suke cikin jam’iyyar suna da yawa, kuma suna da mabambanta ra’ayoyi musamman ganin yadda ake tunkarar shekarar 2023 wadda ita ce za a fafata inda kowace jam’iyya take kokarin kai bantenta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a Jihar Oyo, an yi zabubbukan shugabanni guda biyu na jam’iyyar a birnin Ibadan, yayin da kowane bangare yake ikirarin nasa ne halattaccen shugabanci, wanda daga bisani uwar jam’iyya ta kasa ita ce za ta fayyace su wane ne suke kan daidai, kuma su wane ne suka yi zaben shugabannin kan ka’ida, don haka su za a tabbatar.

Duk da cewar Jam’iyyar PDP ita ce ke mulkin Jihar Oyo amma wannan bai hana ta aukawa cikin matsaloli jingim ba, har ta kai ga an samu zabubbukan shugabanni guda biyu masu hamayya da juna.

To, a cikin Jam’iyyar APC ma haka batun yake.

Jihohin Legas da Kano da Sakkwato da sauransu da dama an yi zabubbukan shugabanni guda biyu yayin da kowane bangare yake ikirarin shi ne halattaccen shugabanci.

Su kuwa jihohi irin su Gombe da Jigawa da Nasarawa an ce an yi zabe lami lafiya ba tare da wata hayaniya mai girman gaske ba.

Amma abin da ya faru a Jihar Kano shi ne kusan abin da ya fi daukar hankali.

A Jihar Kano an samu sababbin shugabannin Jam’iyyar APC guda biyu, inda kowanne yake ikirarin shi ne halattaccen shugaba.

Alhaji Ahmadu Haruna Danzago wanda ya fito daga bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana kansa a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC, yayin da Alhaji Abdullahi Abbas daga bangaren Gwamnan Jihar Kano (Dokta Abdullahi Ganduje) yake ikirarin shi ne sabon shugaban da aka zaba.

Wannan tirka-tirka ta siyasar Kano ta dauki hankalin mutane da yawa kwarai, inda aka samu bangarori biyu masu girman gaske, wato bangaren tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau wanda yake tare da Sanata Barau Jibrin da kuma ’yan Majalisar Wakilai kamar Tijjani Abdulkadir Jobe wanda ya fito mazaba daya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sai kuma Sha’aban Sharada wanda tun da jimawa Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ta kore shi, sai Alhaji Auduwa Gabasawa da Alhaji Haruna Dederi dan majalisa mai wakiltar Karaye da Rogo, wadannan da wadansu su ne tsagin da yake biyayya ga bangaren Malam Ibrahim Shekarau.

Yayin da Sanata Kabiru Gaya da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai Alhaji Alhassan Ado Doguwa da Alhaji Kawu Sumaila da sauran ’yan majalisa kusan 20 suke mara wa bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje baya.

Su dai bangaren Sanata Shekarau sun je har ofishin Jam’iyyar APC na Kasa inda suka mika kokensu ga Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, suna zargin bangaren gwamnati da yin babakere da danne sauran.

Wannan rikici na Jihar Kano, a ganina abubuwa ne uku za su faru.

Na farko, yana da kyau mu fahimci cewa Gwamna Ganduje ba karamin dan siyasa ba ne, ya fi kowa sanin cewa haduwar tsohon Gwamna Kwankwaso da Sanata Shekarau me za ta jawo masa.

Don haka ya fi kowa fahimtar illa da rashin alfanun da waccan haduwa za ta jawo masa shi da gwamnatinsa.

Don haka, abu uku ne zai faru:

  1. Ko dai Ganduje ya ci gaba da rigima da su Sanata Shekarau, har zuwa lokacin da za su ga cewa bukatarsu ba za ta biya ba, su nema wa kansu mafita, shi kuma Gwamna ya kekasa kasa ya ki sauraronsu, ya ki kallon bukatunsu, watakila yana da abin da ya taka zai yi wukar gindi da shi.
  2. Ko bangaren Sanata Ibrahim Shekarau su fi karfin Gwamna Ganduje a Jami’iyyar APC don haka tilas ya sallama musu, ko dai ya bi su a cikin jam’iyyar, musamman idan aka ce uwar jam’iyyar ta kasa ta tabbatar da zaben Danzago a matsayin halattaccen Shugaban Jam’iyyar a Jihar Kano, don haka Gwamna Ganduje ba shi da wata mafita illa ya bi wannan tsari, ko ya fita daga APC ya koma ya hadu da Kwankwaso a PDP, wanda wannan yana da matukar wahala.

Da wuya a yanayin da ake ciki na fuskantar zaben 2023 jam’iyyar ta kware wa Gwamna mai ci baya, duk da cewa irin hakan ta taba faruwa; Domin a sherarar 2018, uwar Jam’iyyar APC ta Kasa ta bayyana bangaren Sanata Aliyu Wamakko a matsayin tsagin da yake rike da jagorancin jam’iyyar a jihar, abin da Gwamna Aminu Tambuwal ya ce ba za ta sabu ba, lamarin da har ta kai shi ga sauya sheka daga jam’iyyar zuwa PDP.

Daukar irin matakin da uwar Jam’iyyar APC ta yi a Sakkwato wanda ya sabbaba mata asarar Gwamna, idan ta dauki irinsa a Kano, to ba shakka irin abin da zai faru ke nan, inda Gwamna Tambuwal ya hadu da tsohon Gwamna Bafarawa a PDP, to irin haka zai iya faruwa, a mance da duk abin da ya faru a hadu da Kwankwaso da Ganduje, wanda yana da kamar wuya.

  1. Ko kuma Ganduje ya sasanta da bangaren su Shekarau domin a ci galaba a kan Kwankwaso, wanda wannan shi na fi zato Gwamna Ganduje zai yi.

Zai yi wahala Gwamna Ganduje ya bari irin wannan rikici ya sabbaba masa asarar mutum irin Sanata Shekarau da dukkan magoya bayansa.

Don haka, tilas a nemo bakin zaren hanyoyin da za a gyara wadannan matsaloli.

Maganin irin duk wannan rikita-rikitar, shi ne a samu dimokuradiyya a cikin jam’iyyu.

Bai wa kowane dan Jam’iyya dama iri daya domin a dama da shi.

Karfakarfa da kama-karya galibi shi yake sabbaba matsaloli irin wadannan, amma idan za a yi adalci, to za a samu saukin fitinu a cikin dukkan jam’iyyun.