✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dimokuradiyyar Najeriya yaudara ce —Tanko Yakasai

Yau Asabar ce Ranar Dimokuradiyya a Najeriya.

Yau Asabar ce Ranar Dimokuradiyya a Najeriya, ranar da ake tunawa tare da murnar ci gaban da dimokuradiyyar ta samar tare da nemo hanyoyin warware matsaloli ko kalubalen da ake ciki.

Aminiya ta zanta da Alhaji Tanko Yakasai da Alhaji Abdulkarim Daiyabu wadanda suka jiya suka ga yau a harkar dimokuradiyyar, inda suka bayyana nasarori da kalubalen da dimokuradiyyar take fuskanta.

Aminiya: A yanzu an kai shekara 22 ana mulkin dimokuradiyya wane ci gaba kake ganin an samu?

Tanko Yakasai: Ni a ra’ayina ban ga wani ci gaba da aka samu wanda yake a bayyane ba, kamar wannan tsawon lokaci da aka dauka ana mulkin dimokuradiyya ba tare da sojoji sun yi katsalanda ba.

Wannan shi ne lokaci na farko da aka samu a tarihin Najeriya. Ana yin zabe ko da gaskiya ko babu.

Ida ana so a kwatanta ci gaban da aka samu a yanzu da kuma baya sai a dauki darajar Naira faduwa ta yi ko sama ta yi, man fetur farashinsa raguwa ya yi ko karuwa ya yi.

To wannan ya ishi mutum ishara ya auna ya ga ci gaba muka samu ko akasin haka don a gaskiya kowa ya san a yanzu ba dimokuradiyya ake yi ba, ana yaudarar kai ne kawai.

Babban akasin da aka samu shi ne an rugurguza dimokuradiyyar kusan ban da neman kudi babu abin da masu mulki suka sanya a gaba.

Idan kwangila ce aka bayar, ana bayarwa ba don a yi wa jama’a aikin ba ko kuma don a buda wa dan kasa hanyar cin abinci ba, ana yi ne don kawai dan kason da shi mai mulkin zai samu ta wannan aiki. Idan ba a bayar da kwangilar ba, ba za a samu wasu kudi da ake son samu ba.

Wane kalubale aka samu?

Wajen tafiyar da mulki ba a yi abin da ya kamata ba. Domin ni na kula cewa ana hawa mulkin ne ba tare da wani shiri ko tsari da za a aiwatar wa al’umma ba.

Abin da ya sa ake yin jam’iyya shi ne don ta zama kamar makaranta ga dan siyasa.

A nan zai koyi yadda zai gudanar da mulki idan Allah Ya sa ya ci zabe. Kowace jam’iyya tana da manufofinta.

Shi kuma dan takarar zai dauko manufofin jam’iyyarsa ya yi yakin neman zabe da su ta hanayar tallata wa al’umma tare da yi musu alkawuran samar musu da abubuwan more rayuwa da suka shafi ilimi da kula da lafiya da hanyoyi da sauransu.

To idan ya samu ya ci zabe wadancan alkawurra da ya yi wa talakawa ko ya fadi a wajen yakin neman zabe, to fa a kansu zai tsara tafiyar da mulkinsa.

Kuma zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya yi abin da ya kamata domin ganin ya sake lashe zabe a nan gaba.

Ya san cewa idan bai yi abin kirki ba, to ba zai samu nasarar cin zabe a gaba ba.

Koda yake abin da ya jawo hakan shi ne yadda talakawa suka zama masu kwadayi ba su nuna damuwarsu ga rashin gudanar da ayyukan da ba a yi musu.

Kasa tana cikin halin rashin tsaro kowa ka gan shi a dimauce a tsorace, domin bai san me zai faru da shi an jima ba.

Kullum kashe rayuka ake yi kamar kiyashi. Tattalin arziki yana cikin wani hali, to ai kin ga wadannan duk kalubale ne da muke fuskanta a yau.

Yaya za a yi a samu mafita?

Muna sa rai nan gaba za a zo lokacin da kan talaka zai waye ya dawo daga rakiyar irin wadancan shugabanni ya kuma rika yin zabe bisa cancanta, ba don kudin da zai samu ba.

Su zabi mutanen da za su yi musu aiki ba wai wanda zai sato kudi ya gutsura musu wani kaso ba.

Su kuma shugabanni za a kawo lokacin da za su san cewa zaben cancanta ake yi don haka dole su dage su yi wa talakawa aiki domin sun san idan ba su yi haka ba, to nan gaba ko suna son tsayawa takara ba za su samu ba.

Ba soja mulkin siyasa ya sa aka rasa dimokuradiyya-Abdulkarim Daiyabu

Aminiya: Shekara 22 ana mulkin dimokuradiyya wane ci gaba aka samu a wannan lokaci?

Duba da yadda na taso na ga siyasa irin tasu Malam Aminu Kano idan ka hada shi da wannan lokaci kai ma ka san babu wani batu na dimokuradiyya.

Kullum ina fadi cewa tun daga lokacin da aka dauki mulkin siyasa aka damka a hannun Cif Obasanjo wanda tsohon soja ne tun daga nan aka rasa dimokuradiyyar.

Mun yi kokarin ganin haka ba ta faru ba, amma saboda kulle-kulle na su Janar Babangida da Janar Abdussalami haka suka shafa wa idonsu toka suka dauko Obasanjo daga kurkuku suka ba shi mulkin kasar nan.

Zan iya tunawa a wancan lokacin ni da su Olu Falae da Umaru Shinkafi muka hada kanmu domin mu kayar da Obasanjo, amma a karshe aka yi amfani da karfin mulki aka ba Obasanjo.

Kafin ya sauka daga mulki sai da ya yi laifi 125 amma ba a tsige shi ba. To daga nan dimokuradiyya ta rasa kimarta.

Haka muka rika tafiya a gurgunce har aka ya kammala lokacinsa na shekara 8.

A yanzu da muka samu Shugaba Muhammadu Buhari mun sa rai za mu samu dimokuradiyya lura da irin halayen kwarai da yake da su da kuma tsarin shugabanci na adalci da ya nuna a lokacin mulkinsa na soja, musamman binciken cin hanci da ya yi a kan gwamnatin Shagari.

Amma abin takaici sai ga shi wadansu miyagu sun kewaye shi sun hana shi gudanar da komai.

Wadanda ke kewayen da shi domin su samu abin da suke so, sai suka fara da sanya masa guba wadda ta janyo masa rashin lafiya.

Abin takaici kuma har yanzu ba a fito an gaya mana su wane ne suka aikata haka ba ballantana a hukunta su.

A bangaren kalubale kuma fa?

Kalubale ai su suka fi yawa. A yanzu da babu jirgin kasa, babu ruwan sha, babu wutar lantarki.

Yanzu idan aka dauki filin jiragen Kano wanda shi ne na farko a kasar nan, ya zama shi ne koma baya. Duk wanda aka dama a je a kashe.

Ina tattalin arziki? Duk mulki ana yin sa ne a kan abubuwa biyar; a kan kare rayuwa da lafiya da dukiya da mutunci da addini.

Masu mulki sun sace dukiyar kasa sun yi kudi sun tsiyata kowa sun bari ana kashe mutane.

To ina zancen dimokuradiyya a nan?

Ai yaudarar kanmu kawai muke yi. Ai irin wannan dimokuradiyyar ma Allah wadarai da ita.

Yaya za a samu mafita daga wannan hali tare da samar da dimokuradiyya ingantacciya?

Kamata ya yi a dawo a yi karatun baya sannan a yi gyara. Lokaci bai kure ba.
Mafita guda daya ce.

Tunda a yanzu mu talakawa mun gane, to abin da ya rage shi ne mu zo mu hada kanmu.

Mu san duk yadda za a yi a kawar da irin wadancan mutane da suka yi barna.

Idan har mutanen banza za su hada kai su cutar da mutanen kirki, to su ma mutanen kirki idan suka hadu za su iya kwatar kansu daga hannun mutanen banza.

Kuma ita gwamnati idan har za ta iya ta zo ta kafa kwamiti mai karfin shari’a da zai binciki tun daga kan gwamnatin Buhari ta mulkin soja har zuwa yau.

Domin Hukumar EFCC tana da rahotannin dukkan barayin shugabannin da suka sace kudin kasar nan suka adana a kasashen waje. Kuma sun san cewa kudin nan ba za a taba dawo mana da su ba.

An samu shugabannin kasa barayi, akwai Abacha loot, akwai batun gonar Obasanjo da dakin karatunsa, akwai batun kudin danyen mai a gwamantin Jonathan.

An samu Shugaban ’Yan sanda barawo, Babban Jojin kasa barawo.

A yanzu kuma an samu rahoton wasu kudade na danyen mai da aka boye a kasashen waje da yawansu ya kai Dala biliyan 69.

Idan aka dawo da su a wannan hali da ake ciki, abin da ake kira ja ya kawo ja ya dauke za a yi.

A fara da kwato waccan dukiya a dawo da ita lalitar kasa sannan a biya diyyar dukkan rayukan da suka salwanta a kasar nan.

Muna kira ga iyaye ko shugabannin al’umma da za su tsaya takara su ji tsoron Allah su kuma malaman addini na kwarai su tsaya su yi musu hudubobi a kan yadda za su jagorancin jama’a ta hanyar adalci da gaskiya.

Su ma sarakuna su zo su bayar da hadin kai tare da tabbatar da komai shugabannin siyasar nan za su yi su yi adalci a ciki.

Shi ya sa dama mu tuntuni muka rungumi Rundunar Adalci.

Ya kasance a zo a gyara duk irin tsarin da muke da shi na zalunci tare da kafa na adalci.

Idan Allah Ya kaddara a cikin shugabannin nan akwai masu rabo suka yi nadama suka koma ga Allah suka dawo da abin da suka yi na barna.

Idan aka zo aka bincika aka kwato duk abin da aka kwato to shi ke nan sai a yi musu afuwa a yi wannan sabuwar tafiya tare.

Amma idan aka bincika aka gano suna da hannu a ciki to sai mu hada su mu yi musu kudin goro mu juya musu baya.

Idan sun shiryu haka muke so, amma idan suka ki ba za mu ci gaba da bin su ba.

Idan mutane kansu ya waye, suka farga, kwadayinsu ya yaye, tsoronsu ya kau, to fa sata ta kare, zalunci ya kare.

Wanda ya yarda da Allah to fa Allah Ya isar masa. Na yi imani duk lalacewar duniya ba a rasa na Allah.

To irin wadannan mutane muke kira su zo su hada kai domin su kwato kansu daga wannan tafiyar ta kura da fatar akuya.