✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Diphtheria: Cutar sarkewar numfashi ta bulla kananan hukumomi 13 a Kano

Gwamnati ta ce za ta gudanar da aikin rigakafi don magance cutar a jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da bullar cutar sarkewar numfashi da ake kira Diphtheria a Kananan Hukumomi 13 na jihar.

Kwamishinan Lafiya na Kano, Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa kan bullar bakuwar cutar da kuma zazzabin Lassa a jihar a ranar Asabar.

Ya ce an samu akalla mutum 100 da ake zargin sun kamu da cutar inda uku daga cikinsu suka mutu.

“Ya zuwa ranar 20 ga watan Janairu, 2023, mun samu rahoton mutum 100 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi 13.

”Kananan hukumomin su ne Ungogo, Nassarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Karamar Hukumar Birni, Kumbotso, Kiru, Rano, da kuma Gwarzo.

“A cikin mutum 100 da ake zargin sun kamu, an tabbatar da harbuwar takwas daga cikinsu, yayin da muke jiran karin sakamako.

“Mun rasa rayukan mutum uku daga cikin takwas da aka tabbatar sun kamu da cutar.”

Tsanyawa, ya ce a halin yanzu mutum 27 ne suke karbar magani yayin da 41 kuma aka sallame su.

Kwamishinan ya bayyana cewa, a ranar 10 ga watan Janairu, Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kiwon Lafiya ta samu rahoton wani da ake zargin yana dauke da cutar zazzabin Lassa a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano.

Ya ce an tura wata tawaga domin gudanar da bincike, inda aka gudanar da gwaje-gwaje sannan bayan kwana uku sakamakon ya nuna yana dauke da zazzabin Lassa.

“An yi wa mutum 10 gwaji daga cikin wadanda ke da hatsarin kamuwa da cutar, uku sun kamu da cutar, wanda adadinsu ya kai hudu kuma a halin yanzu ana ba su kulawa a asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano,” in ji Tsanyawa.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano ta bude cibiyar killace masu cutar zazzabin Lassa ta Kwanar Dawaki.

Ya kara da cewa an horar da ma’aikatan kiwon lafiya tare da tura su cibiyar.

Ya yi nuni da cewa jihar za ta gudanar da aikin rigakafi na yau da kullum a kananan hukumomin da abin ya shafa.