Direba ya guntule tare da hadiye yatsan ma’aikacin gwamnati a Ebonyi | Aminiya

Direba ya guntule tare da hadiye yatsan ma’aikacin gwamnati a Ebonyi

Kisa
Kisa
    Muhammad Auwal Suleiman

Wani direban motar kabu-kabu da ba a bayyana sunansa ba,  ya guntule wa kuma ya hadiye yatsan Iboko Kenneth, ma’aikacin Hukumar Raya Biranen Jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne bayan wata takaddama da ta barke ranar Talata tsakanin direban da Iboko wanda ke aikin wucin gadi da hukumar raya birnin a banagaren kula da ababen hawa.

Kwamishinan Hukumar Raya Biranen Jihar, Cif Onyekachi Nwebonyi, ya bayyanawa ’yan jarida a Abakaliki cewa wannan aika-aikar da direban ya yi abin takaici ne, inda ya yi  tir tare da Allah wadai da hakan.

A cewarsa, abin bakin ciki ne a ce direba ya yi fada da jami’in dake kokarin sanya birninJjihar a kan tsari, kuma har takai ga ya gutsure mishi yatsa ya kuma cinye.

Tuni dai aka garzaya da jami’in sashen bayar da agajin gaggawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Alex Ekwueme da ke  Abakaliki domin samun kulawa.