✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direba ya mutu a cikin tankin tankar mai a Kano

Direban ya gamu da ajalinsa bayan ya makale a cikin tankin motar.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani direban tankar mai mai shekara 45, Dahiru Aliyu a unguwar Hotoro.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, shi ne ya fitar da sanarwar faruwar lamarin a ranar Talata.

“Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin.

“Mun samu kiran wayar neman agaji daga wani mai suna Shuaibu Muhammad da misalin karfe 10:59 na safe, kuma take muka tura jami’anmu zuwa wajen da abun ya faru,” a cewarsa.

Ya kara da cewa, Aliyu ya shiga cikin tankin tankin motar ce domin wanke man da ke ciki, amma aka yi rashin sa’a ya makale a ciki har ya mutu.

“Tankar man na dauke da lambar DLD 411 XF,” inji Abdullahi.