✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Direban Shugaba Buhari ya riga mu gidan gaskiya

Sa’idu Afaka ya rasu a Asibitin Fadar Shugaban Kasa bayan ya yi jinya mai dogon zango.

Direban Shugaba Muhammadu Buhari, Sa’idu Afaka, ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Fadar Gwamnatin Najeriya ta tabbatar.

Sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta ce Afaka ya rasu ne da yammacin Talata a Asibitin Fadar Shugaban Kasar da ke babban birnin Tarayya.

Malam Garba ya ce mai gidansa yana mika sakon ta’aziya ga iyalan mamacin wanda ajali ya katse masa hanzari bayan kwanciya jinya ta tsawon lokaci.

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana mika sakon ta’aziyya ga iyala direbensa, Sa’idu Afaka wanda ya rasu ranar Talata a Asibitin Fadar Gwamnatin Najeriya bayan doguwar rashin lafiya.”

“Shugaba Buhari yana kuma jajantawa Gwamnati da jama’ar Jihar Kaduna dangane da wannan rashi,

“Ya bayyana Marigayi Afaka a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana wanda ya tafiyar da aikinsa cikin matukar kulawa,” a cewar sanarwar.

Malam Shehu ya kara da cewa, Shugaba Buhari yana tuna lokacin da Marigayi Afaka ya tsinci wata jaka cike da makudan kudi a shekarar 2016, yayin da ya je sauke farali a kasa mai tsarki kuma ya mika wa Hukumar Alhazai domin a jigita mai ita.

Ya ce, wannan kyakkyawar dabi’a ta gaskiya ta janyo masa yabo da jinjina daga hukumomin Saudiya da na Najeriya.

Mutuwar Sa’idu na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Buhari ke ganin likitocinsa a birnin Landan.